Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-10-11 16:15:21    
Za a ci gaba da raya dangantakar aminci tsakanin kasashen Zambia da Sin, in ji ministan harkokin waje na Zambia

cri
Bayan da sabon ministan harkokin waje na kasar Zambia Mundia Sikatana ya yi rantsuwar kama aiki a fadar shugaban kasar a ran 10 ga wata, ya yi jawabi ga kafofin watsa labaru, inda ya ce, kasar Zambia za ta ci gaba da kiyayewa da kuma bunkasa dangantakar aminci da ke tsakaninta da kasar Sin.

Lokacin da yake tufa albarkacin baki kan taron koli na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka da za a yi a birnin Beijing a wata mai zuwa, Mr. Sikatana ya bayyana cewa, idan lokacin ya yi, shugaban kasar Zambia Levy Mwanawasa zai zo birnin Beijing, babban birnin kasar Sin don halartar taron tare da wasu ministocin gwamnatin kasar Zambia. Ban da wannan kuma ya ce, gwamnatin kasar Zambia tana dora muhimmanci sosai kan taron, kuma tana fatan za ta bayar da gudummuwarta ga taron.

Bugu da kari kuma, Mr. Sikatana ya nuna cewa, kasar Zambia tana son ci gaba da karfafa hadin gwiwa tsakaninta da kasar Sin a fannin tattalin arziki, kuma ana fatan kamfanonin kasar Sin da yawa za su je Zambia domin zuba jari.(Kande Gao)