Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-10-10 17:59:33    
Firayin ministan kasar Habasha ya gana da mai ba da taimako ga ministan harkokin waje na kasar Sin

cri
A ran 9 ga wata, a birnin Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha, Meles Zenawi, firayin ministan kasar ya gana da Zhai Jun, babban sakataren kwamitin share fage ga taron koli na Beijing na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka kuma mai ba da taimako ga ministan harkokin waje na kasar Sin, inda ya bayyana cewa, taron koli na Beijing da kuma taron ministoci karo na uku na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka da za a yi wani gagarumin taro ne da ke da tasiri sosai, wanda zai bude wani sabon shafi na dangantakar hadin kai ta aminci da ke tsakanin Sin da Afirka.

Mr. Meles ya nuna gamsuwa sosai ga ayyukan share fage ga dandalin, kuma ya ce, bisa matsayinta na wata kasar da ke shugabantar taron tare, kasar Habasha za ta bayar da gudummowarta ga budewar taron cikin nasara.

Daga nasa bangare, Zhai Jun ya bayyana cewa, taron koli na Beijing na dandalin wani muhimmin taro ne a cikin tarihin dangantakar aminci tsakanin Sin da Afirka, kuma tabbas ne zai yi tasiri ga hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka daga dukkan fannoni.

Ban da wannan kuma Mr. Meles ya nuna godiya ga kasar Sin da ta samar da taimakon kyauta ga bunkasuwar tattalin arzikin kasar Habasha. Kuma ya bayyana cewa, kasashen Habasha da Sin su sahihan aminai ne, bangaren Habasha zai yi kokari tare da bangaren Sin domin sa kaimi ga bunkasuwar dangantakar da ke tsakaninsu daga dukkan fannoni.(Kande Gao)