Yayin da shugaban kwalejin nazarin huldar da ke tsakanin kasa da kasa ta kasar Kamaru ke hira da manema labaru na kasar Sin a kwanan baya, ya ce, 'ina fatan kasar Sin za ta kara baiwa Kamaru taimako a fannin fasahohi, kuma ina fatan za a tsara hakikanin shiri na ba da taimakon.'
Ya ce, tun bayan da aka kulla huldar diplomasiyya a tsakanin Kamaru da Sin, huldar da ke tsakanin kasashen biyu ta yi ta bunkasa lami lafiya, kuma an yi ta inganta hadin gwiwar da ke tsakaninsu, kasar Sin ta bayar da babban taimako da tallafin fasaha ga kamaru a fannin bunkasuwar tattalin arzikinta. Game da taron dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka da za a yi a watan Nuwamba mai zuwa a nan birnin Beijing, ya jaddada cewa, kara tabbatar da ayyukan hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka a hakika, zai zama babban makasudin Kamaru a wajen halartar taron nan. Ban da wannan, ya kuma yi fatan taron zai zama wani dandalin da za a inganta hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka da kuma Sin da Kamaru daga dukan fannoni.(Lubabatu)
|