Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-09-18 18:32:01    
Kasar Sin tana yin kokari domin kyautata sharudan kiwon lafiya na yankunan da ke fama da talauci

cri

A yankunan da ke fama da talauci na kasar Sin, matsalar da mazaunan wuraren suka fi fuskanta ita ce kamuwa da ciwace-ciwace, sabo da Mutane da yawa ba su da kudin ganin likita.

Tare da bunkasuwar tattalin arziki da zamantakewar al'umma ta kasar Sin a cikin shekarun nan da suka gabata, gwamnatin kasar Sin tana ganin cewa, kara zuba jari a fannin kiwon lafiya yana da muhimmanci sosai, haka kuma yana yin kokari don kyautata harkokin kiwon lafiya na yankunan da ke fama da talauci na kasar Sin. Ba da dadewa ba, wakilinmu ya ziyarci gundumar Pan ta jihar Guizhou, wani yankin da ke fama da talauci a kudu maso yammnacin kasar Sin domin fahimtar halin da wurin ke ciki kan kiwon lafiya. To, a cikin shirinmu na yau, za mu ji bayanin da wakilinmu ya ruwaito mana daga gundumar Pan.

Gudumar Pan ta jihar Guizhou tana kudu maso yammacin kasar Sin, kuma tana daya daga cikin gundumomi 600 wadanda gwamnatin kasar Sin ta tabbatar wajen taimake su don fama da talauci. Wannan ya nuna cewa, gundumar Pan wuri ne mafi talauci a kasar Sin. Matsakaicin yawan kudin da ko wane mutumin wurin ya samu daga aikin kawo albarkar kasa ya kai kimanin dala 500, wato ke nen ya kai rabi na matsakaicin yawan kudin da ko wane mutum ya samu a duk fadin kasar Sin. Haka kuma sabo da talauci, fararren hula masu yawa na wurin ba su da kudin ganin likita. Domin magance matsalar, a shekara ta 2005, an fara tafiyar da tsarin jiyya na hadin gwiwa na kauyuka irin na sabon salo a gundumar Pan. Shugaban gundumar Luo Zixiang ya bayyana cewa,

"An mayar da gundumar Pan a matsayin gundumar gwaje-gwaje kan tsarin jiyya na hadin gwiwa na kauyuka irin na sabon salo. Dalilin da ya sa gwamnatin kasar Sin ta tsara wannan manufa shi ne sabo da tana so ta magance matsalar sake shiga talauci sakamakon kashe kudi wajen jiyya da fararren hula suke fuskantar. Fararren hula sun nuna goyon baya sosai ga wannan manufa, kuma dukkansu suna ganin cewa, wannan wata manufa ce da ke kawo musu alheri."

Tsarin jiyya na hadin gwiwa na kauyuka iri na sabon salo wani tsari ne da gwamnatin kasar Sin ta bullo da shi domin kyautata harkokin kiwon lafiya na kauyukan kasar Sin, wato a ko wace shekara, gwamnatin kasar Sin tana bayar da taimakon kudi yuan 20 ga ko wane dan kauye da ke shiga tsarin, gwamnatocin yankuna sun bayar da taimakon kudi yuan 20, kuma farerran hula sun ba da kudi yuan 10, daga baya kuma an tattara wadannan kudadde tare don kafa asusun jiyya na hadin gwiwa. Idan 'yan kauye suka kamu da ciwo, to suna iya gabatar da rasidi kan kudin da suka kashe wajen jiyya domin a mai da musu kudaden da suka kashe. Sabo da haka an magance matsalar rashin kudin ganin likita da 'yan kauye suke fuskantar bisa wani matsayi. Ya zuwa yanzu, 'yan gundumar Pan da yawansu ya kai kashi 87.5 cikin dari sun riga sun shiga tsarin jiyya na hadin gwiwa.

Ko da yake an riga an warware matsalar, amma har yanzu babu isassun kayayyakin jiyya da kararrun likitoci da kuma sauran matsaloli suna yin mumunar illa ga lafiyar mazaunan wurin. Madam Zhang Yaling, wata nas ta asibitin kauyen Machang na gundumar Pan ta bayyana cewa, yanzu mutane da yawa suna zuwa asibiti don ganin likita, shi ya sa matsalolin rashin fasahohin zamani da ingantattun kayayyakin jiyya da likitoci da nas-nas suna tsananta.

" Muna iya warkar da wasu ciwace-ciwace wadabda va sy tsababta ba kamar mura, amma idan an kamu da ciwo mai tsanani, sai za mu ba da shawarar zuwa asibitin da ke cikin gudumar don ganin likita. Yanzu muna da wata na'urar zamani domin gano cuta a jikin mutum, amma ba mu iya yin amfani da ita ba. Kuma dukkanmu muna fatan za mu iya zuwa sauran wurare domin kara ilminmu."

Ban da wannan kuma wakilinmu ya gano cewa, akwai wasu kananan dakunan shan magani da ba na gwamnati ba a gundumar Pan. Wadannan dakunan shan magani sun iya bayar da gudummowa ga hukumomin jiyya na gwamnati, idan 'yan kauye sun kamu da wasu ciwace-ciwace marasa tsanani, ya fi kyau sun je irin wadannan dakunan shan magani da ba na gwamnati ba, amma yanzu dakunan shan magani su ma suna fuskantar matsalar kudi. Wang Qing wanda ke gudanar da dakin shan magani da ba na gwamnati ba har shekaru 10 ya ce,

"Tattalin arziki na wurin yana baya sosai, shi ya sa fararren hula masu yawa ba su da kudin ganin likita. Na kan gamu da irin wannan hali, wato wasu mutane sun kamu da ciwon huhu, kuma zafin jikinsu ya kai digiri 39 ko 40 sakamakon zazzabi, sun zo dakina don ganin likita, amma suna da kudi kadan. Ba yadda za a yi sai na ba su magani. Ya zuwa yanzu mutane da yawa ba su ba ni kudi ba."

Mr. Wangqing yana fatan gwamnatin wurin za ta iya gano cewa, dakunan shan magani da ba na gwamnati ba suna ba da taimako ga hukumomin jiyya na gwamnati, sabo da haka za ta nuna musu goyon baya.(Kande Gao)