Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-09-13 15:45:45    
Akwai abubuwa da yawa na babban taron MDD da ke jawo hankulan jama'a

cri

A ran 12 ga wata, an bude babban taro na karo na 61 na majalisar dinkin duniya a hedkwatar majalisar dinkin duniya da ke a birnin New York na kasar Amurka. Ban da batutuwa da a kan tattauna a gun irin wannan babban taro, kuma akwai sauran batutuwa da ake tattaunawa a gun wannan babban taro, dangane da kara aiwatar da " yarjejeniyar sakamako" da aka cimmawa a gun taron shugabannin duniya, da zaben babban sakataren majalisar dinkin duniya da matsaloli masu tsanani na yankuna. Ka zalika Madam Sheikha Haya Rashed Al Khalifa, shugabar wannan babban taron majalisar dinkin duniya kuma alkalin kasar Bahrain ta zama mata ta farko da aka zaba don ta zama shugabar babban taron majalisar dinkin duniya a cikin shekaru 36 da suka wuce, duk wadannan sun jawo hankalun kasashe daban daban.

A lokacin da aka yi babban taro na karo na 60 na majalisar dinkin diniya a shekarar bara, an taba shirya taron shugabannin kasashen duniya, sabo da haka ba a nuna kulawa sosai ga matsalolin duniya da yawa ba. Amma tun bayan watun Yuli da ya wuce, sai wadannan matsaloli na kara jawo hankulan duniya sannu a hankali, kamar batun yin kwaskwarima kan majalisar dinkin duniya, da samun bunkasuwa, da kuma yaki da ta'adanci. Haka nan kuma yanzu lokaci ne mai matukar muhimmanci ga daidaita batun nukiliyar kasar Iran da na yankin gabas ta tsakiya da yankin Darfur na kasar Sudan da sauran manyan batutuwa masu yawa. Kasashe daban daban suna mai da hankulansu sosai ga duk wadannan batutuwa. Don haka ko shakka babu, batutuwan nan za su zama batutuwa da za a fi tattaunawa a gun babban taro na shekarar nan. Bisa farkon kidayar da majalisar dinkin duniya ta yi, an ce, akwai batutuwa sama da 150 wadanda za a tattauna a gun babban taron, wadanda kuma suka shafi zaman lafiya da kwanciyar hankali, da bunkasuwa, da hakkin dan adam, da ayyukan ba da agajin jin kai, da gaggauta kafa tsarin dokoki, da yaki da ta'addanci, da kwance damara, da tsarin hukumomin majalisar dinkin duniya da dai sauransu.

An kiyasta cewa, yawan shugabannin kasashe daban daban da na gwamnatocinsu wadanda za su halarci babban taron majalisar dinkin duniya na shekarar nan zai wuce 80. Mr Li Zhaoxing, ministan harkokin waje na kasar Sin zai yi jawabi a gun taron, inda zai bayyana matsayin gwamnatin kasar Sin a kan manyan batutuwan duniya da dama.

Mr Kofi Annan, babban sakataren majalisar dinkin duniya wa'adin aikinsa zai cika a karshen shekarar nan. Yanzu, kasashen Asiya biyar kamar Korea ta Kudu da Thailand da Sri Lanka da Indiya da Jordan sun yi rijistar sunayen mutanensu don shiga takarar zaman sabon babban sakataren majalisar. An ruwaito cewa, mai yiwuwa ne, sauran kasashe su ma za su gabatar da mutanensu don tsayawa takarar.

Madam Khalifa, ita ce mata ta uku da ta zama shugabar babban taron majalisar dinkin duniya. An lura da cewa, a cikin jawabin da ta yi a gun bikin bude babban taron, Madam Khalifa ta bayyana cewa, ya kamata, majalisar dinkin duniya ta kara taka rawarta, babban taron majalisar yana bukatar ci gaba da yin gyara, kuma wajibi ne, ta tsara shirin daidaituwa domin fuskatar babban kalubale a yanzu, amma babu yadda za a yi an cimma wannan, sai a gudanar da manufar rukunoni da dama.

Da Madam Khalifa ta tabo magana a kan batun yaki da ta'addanci, sai ta bayyana cewa, yaki da ta'addanci a duniya wani aiki ne mai wuya sosai. Wajibi ne, gamayyar kasa da kasa ta dauki matakai wajen yaki da ta'addanci don yin rigakafi da dagiya. Ta kara da cewa, an zartas da "manyan tsare-tsaren yaki da ta'addanci a duk duniya" a gun babban taro na karo na 60 na majalisar dikin duniya, tana fatan duk kasashen majalisar da su kara kokari wajen cim ma yarjejeniyar yaki da ta'addanci daga duk fannoni a gun wannan babban taron majalisar. Yanzu bangarori daban daban suna mai da hankaluna sosai ga yadda za a aiwatar da wadannan ra'ayoyi da Madam Khalifa ta gabatar. (Halilu)