Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-09-13 14:38:24    
Labarun wasannin motsa jiki(07/09-13/09)

cri

Jama`a masu sauraro,barkanku da war haka,barkanmu da sake saduwa da ku a cikin shirinmu na yau na `wasannin motsa jiki`,wanda mu kan gabatar muku a ko wace ranar Laraba.Da farko dai,za mu karanta muku wasu labarun wasannin motsa jiki,daga baya kuma sai wani bayanin musamman.

1)A ran 6 ga wata,a babbar ganuwa ta `Badaling` ta birnin Beijing,an yi nune-nunen abun nuna fatan alheri na taron wasannin Olimpic na nakasassu na Beijing na shekara ta 2008 wato karamin sa da ake kiransa da suna `lele`,dalilin da ya sa aka zabe sa da ya zama abun nuna fatan alheri shi ne domin bisa al`adar gargajiyar kasar Sin,ma`anarsa ita ce kwazo da himma da kuma kokari,wannan ya dace da tunanin taron wasannin Olimpic na nakasassu da za a yi daga ran 6 zuwa ran 17 ga watan Satumba na shekara ta 2008 a birnin Beijing.

2)A ran 5 ga wata,a birnin Beijing,mataimakiyar shugaban zartaswa ta kwamitin shirya taron wasannin Olimpic na Beijing madam Tang Xiaoquan ta bayyana cewa,ana tsarawa gine-gine masu saukin hawa ga nakasassu a cikin filaye da dakuna na taron wasannin Olimpic na Beijing.Madam Tang ta ci gaba da cewa,aikin da ake yi yanzu zai biya bukatun kwamitin wasannin Olimpic na nakasassu na duniya.Ban da wannan kuma ana yin gyara kan mafitar tashar jirgin kasa dake karkashin kasa musamman domin nakasassu.

3)A ran 10 ga wata,an rufe budaddiyar gasar kwallon tebur ta kasar Singapore ta shekara ta 2006,a gun gasar da aka yi,kungiyar kasar Sin ta sami dukkan zakaru hudu,wadanda a ciki `dan wasa Ma Lin ya zama zakara na maza,`yar wasa Zhang Yining ta zama lambawan ta mata.

4)A ran 9 ga wata,a birnin Stuttgart na kasar Jamus,an yi gasa ta karshe ta gasar ba da babbar kyauta ta guje-guje da tsalle-tsalle ta hadaddiyar kungiyar guje-guje da tsalle-tsalle ta duniya ta shekara ta 2006,`dan wasa na kasar Sin Liu Xiang ya sami lambawan a cikin gasar gudun tsallake shinge na mita 110 bisa maki na dakika 12 digo 93,kuma ya karya matsayin bajimta na gasar nan.

5)A ran 9 ga wata,an kawo karshen gasa ta karshe ta gasar cin kofi ta wasan kwallon kwando ta samari ta Asiya ta 19 a birnin Wulumuqi dake yammacin kasar Sin,kungiyar kasar Sin ta lashe kungiyar kasar Korea ta kudu kuma ta zama zakara.

6)A ran 10 ga wata,an kammala gasar karshe ta gasar ba da babbar kyauta ta wasan kwallon hannu ta mata ta duniya ta shekara ta 2006 a birnin Reggio Calabria dake kudancin kasar Italiya.Kungiyar kasar Brazil ta lashe kungiyar kasar Rasha da maki 3 bisa 1,ta zama zakara,wato wannan ne karo na uku da ta rike da zaman lambawan a cikin wannan gasa.Kungiyar kasar Sin ta zama lamba ta biyar.