Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-09-08 10:20:58    
An yi kira ga kasar Iran da ta bayyana ra'ayi mai yakini kan batun nukiliya na kasar

cri
A ran 7 ga wata, a birnin Berlin na kasar Jamus, wakilan kasashen Amurka da Birtaniya da Faransa da Rasha da Sin da kuma Jamus sun kira taro kan batun nukiliya na kasar Iran a asirce, inda suka yi kira ga kasar Iran da ta bayyana ra'ayi mai yakini kan matsalar nukiliya. A ranar kuma, Kofi Annan da shugabannin kasashen Spain da Faransa sun yi bayani bi da bi cewa, ya kamata a warware batun nukiliya na Iran ta hanyar yin tattaunawa da shawarwari.

Zhang Yan, shugaban sashen kula da harkokin soja na ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin wanda ke halartar taron ya bayyana cewa, ana kasancewar sabanin da ke tsakanin bangarori daban daban kan batun sanyawa Iran takunkumi. Amma dukkan wakilan kasashen shida sun nuna goyon baya ga shawarwarin da za a yi tsakanin Javier Solana, babban wakilin kungiyar EU mai kula da manufofin diplomasiyya da tsaron kai da Ali Larijani, wakili na farko na kasar Iran kan yin shawarwari dangane da nukiliya a ran 9 ga wata.

Ban da wannan kuma Mr. Zhang Yan ya ce, a ciki halin da ake ciki yanzu, bangaren Sin yana tsayawa kan ra'ayin warware batun nukiliya na Iran ta yin tattanawa da shawarwari, kuma yana fatan Iran za ta bayyana ra'ayi na hadin gwiwa.(Kande Gao)