Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-09-07 19:54:46    
Kasar Sin ta riga ta yanke shawarar ci gaba da girke bataliyar sojojin injiniyoyi ta kasar Sin a cikin rundunar sojojin kiyaye zaman lafiya da MDD take girke a kasar Lebanon

cri

A gun wani taron manema labaru da aka shirya a ran 7 ga wata a birnin Beijing, kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin Qin Gang ya bayyana cewa, kasar Sin ta riga ta yanke shawarar ci gaba da girke bataliyar sojojin injiniyoyi ta kasar Sin a cikin rundunar sojojin kiyaye zaman lafiya da MDD take girke a kasar Lebanon.

Mr Qin ya ce, bayan da kwamitin sulhu na MDD ya zartas da kuduri mai lamba 1701, an samu sassauci game da halin da ake ciki tsakanin Lebanon da Isra'ila. Amma kasar Sin tana ganin cewa, yanzu wannan halin tsagaita bude wuta ba shi da inganci, kuma ya kasance da wasu dalilai da ba a san su ba.

Mr Qin ya ci gaba da cewa, aikin gaggawa shi ne kamata ya yi a karfafa sojojin kiyaye zaman lafiya na MDD kuma a girke su a kasar Lebanon tun da wuri. Kasar Sin ta riga ta yanke shawarar ci gaba da girke bilitaniyar sojojin injiniyoyi ta kasar Sin a cikin rundunar sojojin kiyaye zaman lafiya da MDD take girke a kasar Lebanon, kuma za a canza su yadda ya kamata.

Game da MDD ta kara tura sojoji zuwa kasar Lebanon, wannan kakaki ya ce, hukumomin da abin ya shafa na kasar Sin suna yin nazari cikin yakini.(Danladi)