Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-09-07 11:02:02    
(sabunta)An jinkirtar lokacin yin shawarwari tsakanin Solana da Larijani

cri
A ran 6 ga wata, zaunannen wakilin kasar Iran da ke hukumar makamashin nukiliya ta duniya Aliasghar Soltanieh ya tabbatar da cewa, an jikirtar lokacin yin shawarwari tsakanin Ali Larijani, wakili na farko na kasar Iran a kan shawarwari dangane da batun nukiliya da Javier Solana, babban wakilin kungiyar EU mai kula da manufofin diplomasiyya da tsaron kai bisa wani dalili, wanda aka tsai da yinsa a ran 6 ga wata.

A ranar, ministan harkokin waje na kasar Iran Manouchehr Mottaki ya nanata a birnin Teheran, babban birnin kasar Iran, cewa kasar Iran tana yin ayyukan nukiliya ne bisa makasudin zaman lafiya, kasar Amurka tana yunkurin sanyawa kasar Iran takunkumi maras adalci ta hanyar kwamitin sulhu na MDD da sauran kungiyoyin duniya, amma wannan yunkuri ba zai samu nasara ba.

Haka kuma a ran 6 ga wata, Robert Joseph, mataimakin sakataren harkokin waje na kasar Amurka mai kula da yin amfani da makamai da harkokin tsaron kai na kasashen duniya ya bayyana cewa, kasashen duniya ba su amince Iran ta mallaki makaman nukiliya ba, wajibi ne kwamitin sulhu na MDD ya sanya wa Iran takumkumi.(Kande Gao)