Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-09-06 21:25:21    
An jinkirtar lokacin yin shawarwari da ke tsakanin Solana da Larijani

cri

A ran 6 ga wata, wakilin kasar Iran da ke hukumar makamashin nukiliya ta duniya Aliasghar Soltanieh ya tabbatar da cewa, an jinkirtar lokacin yin shawarwari da ke tsakanin Javier Solana, babban wakilin kungiyar Eu mai kula da manufofin diplomasiyya da tsaron kai da Ali Larijani, wakili na farko na kasar Iran a kan yin shawarwari dangane da nukiliya bisa wani dalili.

Bisa shirin da aka yi a da, ya kamata Mr Solana da Larijani su yi shawarwari a ran 6 ga wata a birnin Vienna, domin karin haske a kan amsa da kasar Iran ta bayar game da shirin da kasashe shida suka gabatar. Bayan haka, zaunannun jami'an diplomasiyya na zaunannun mambobin kasashe 5 na kwamitin sulhu na MDD da na Jamus za su yi shawarwari a birnin Berlin domin kimanta sakamako da Mr Solana da Larijani suka samu domin tabbatar da matakai da za a dauka a kan kasar Iran.

A ran nan a birnin Tehran, ministan harkokin waje na kasar Iran Manouchehr Mottaki ya sake nanata cewa, kasar Iran tana aikin nukiliya ne bisa makasudin zaman lafiya, kuma yana fata kada kasar Amurka ta sake daukar matakai a kan kasar Iran kamar yadda ta yi a da.(Danladi)