Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-09-06 11:29:26    
Kasar Amurka da KKT suna tsayawa kan matsayi iri daya kan batun nukiliya na kasar Iran

cri
A ran 5 ga wata da dare, zaunannen wakilin kasar Amurka da ke hukumar makamashin nukiliya ta duniya Gregorya Schulte ya bayyana cewa, kasar Amurka da kungiyar gamayyar Turai suna tsayawa kan matsayi iri daya kan batun nukiliya na kasar Iran. A ranar kuma, mai ba da taimako ga shugaban kasar Rasha Igor Shuvalov ya bayyana a birnin Moscow, babban birnin kasar Rasha cewa, mai yiyuwa ne kasar Rasha za ta sa hannu a yunkurin sanyawa kasar Iran takunkumi.

Mr. Schulte ya bayyana a ran nan da dare, cewa idan kasar Iran ba ta son dakatar da ayyukanta na tace sinadarin Uranium ba, to kwamitin sulhu na MDD zai tattauna kan batun sanya mata takunkumi. Ban da wannan kuma ya ce, kasar Amurka da kungiyar tarayyar Turai dukkansu suna son warware batun nukiliya na Iran ta hanyar diplomasiyya, a waje daya kuma suna tsayawa kan matsayi iri daya kan batun ko za a yi sanyawa Iran takunkumi ko a'a, wato dukkansu sun amince da cewa, ya kamata matakin da za a dauka kan batun nukiliya na Iran ya kunshi abubuwan da ke dangane da sanyawaIran takunkumi.(Kande Gao)