Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-08-30 14:43:46    
Kofi Annan ya yi kira ga kasar Isra'ila da ta kawo karshen kawanyat da take yi wa kasar Lebanon ba tare da bata lokaci ba

cri

Ran 29 ga wata a Jelusalem, Kofi Annan, babban sakataren M.D.D., wanda ke yin ziyara a kasar Isra'ila ya tattauna da Amir Perez, ministan tsaron kasar Isra'ila, bayan haka kuma ya bayyana cewa, yana fata kasar Isra'ila za ta kawo karshen kawanyar da take yi wa kasar Lebanon ba tare da bata lokaci ba, domin kafa wani hali mai kyau wajen sake gina kasar Lebanon bayan yaki.

Bayan haka kuma, Mr. Annan ya nuna cewa, tun bayan da aka soma yi amfani da kuduri mai lamba 1701 na kwamitin sulhu na M.D.D. a ran 14 ga wata, ya kamata kasar Isra'ila ta dauki nauyi kan yawancin lamuran da suka karya kudurin. Mr. Peretz ya bayyana cewa, kasar Isra'ila tana fatan kawo karshen kawanyar da take yi wa kasar Lebanon a 'yan kwanaki masu zuwa, amma bai bayyana hakikanin lokaci ba.

A wannan rana kuma a garin Naqoura da ke kudancin kasar Lebanon, Mr. Annan ya yi wani jawabi, inda ya karfafa yin kira ga bangarori daban daban da ke da nasaba da su bi kuduri mai lamba 1701 na kwamitin sulhu. Ya nuna cewa, ayyukan kawanyar da daga teku da sama abubuwa masu kunya ne ga kasar Lebanon, su ne kuma ayyukan kai hari ga yancin kan Lebanon. (Bilkisu)