Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-08-28 17:42:08    
Takaddamar dake tsakanin Kasar Iran da kasar Amurka ta kara tsananta

cri

Wakilin Rediyon kasar Sin ya aiko mana labari cewa , a ran 8 ga watan jiya , Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya zartas da kuduri mai lamba 1696 , inda ya nemi kasar Iran da ta daina aikin inganta uranium kafin ran 31 ga watan Agusta . Sabo da ake kusa da wannan rana , takaddamar dake tsakanin Kasar Iran da kasar Amurka ta kara tsanani .

A ran 26 ga watan nan a birnin Teheran , hedkwatar kasar Iran , wata Ma'aikatar gyare-gyaren Heavy water wato ruwa mai nauyi ta fara aiki , kuma kasar Iran tana rawar daji . Bugu da kari kuma sojojin ruwa na kasar Iran sun harbi wani makami mai linzami mai dogon zango a ran 27 ga watan Agusta . Saboda haka , bangaren kasar Amurka ya ce , idan a ran 31 ga watan nan Kasar Iran ba za ta daina aikin inganta uranium ba , to , kasar Amurka za ta dauki matakin yin takunkumi kan kasar Iran ta hanyar kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya . Idan wannan aiki ya ci tura , to , kasar Amurka za ta kafa wata kungiyar tarayya don yin takunkumi kan kasar Iran .

Amma duk da haka , ELHam , kakakin Ma'aikatar harkokin waje ta kasar Iran ya ce , Ahmadi Nejad , shugaban kasar Iran ya rubuta wasika ga shugaba Bush na kasar Amurka , inda ya gabatar da sabon shiri kan warware matsalar duniya da sassauta hali mai tsanani na duniya na yanzu . Wannan wasika ta farko ce da shugaban kasar Iran ya rubuta wa shugaban kasar Amurka a cikin shekaru fiye da 20 da suka shige bayan da kasashen biyu suka yanke huldar diplomasiya .

A gun wani taron watsa labaru da aka shirya a wanmnan rana , Mr. Elham ya bayyana cewa , Manoucher Mottaki , ministan harkokin waje na kasar Iran ya roki Jakadan kasar Swess dake kasar Iran da ya yi 'dan bayani kan wannan wasikar lokacin da ya mika wasikar zuwa ga bangaren Amurka . Ya ce , a cikin wasikar , shugaban kasarsa ya gabatar da sabon shiri kan warware matsalar duniya da sassauta hali mai tsanani na duniya na yanzu . Amma bai bayyana cewa , wannan wasikar ko ta shafi matsalar nukiliyar kasar Iran ba. A wannan rana , Mr. Mottaki , ministan harkokin waje na kasar Iran ya gaya wa manema labaru cewa , mai yiwuwa ne wannan wasikar za ta kawo sabuwar damar diplomasiya , amma wannan ba ya nufin cewa , kasar Iran ta sassauta matsayinta kan matsalar nukiliya .

Masu nazarin al'amuran duniya suna ganin cewa , a cikin 'yan kwanakin da suka shige , kullum kasar Iran tana son yin shawarwarin kai tsaye da kasar Amurka . Wasikar shugaban kasar Iran ta bayyana wannan nufi sosai . Kasar Iran tana ganin cewa , ba Kungiyar Tarayyar kasashen Turai ba , kuma ba Hukumar makamashin nukiliya ta duniya ba , kasar Amurka ce kawai za ta tsai da kuduri kan matsalar nukiliya .

A gun taron watsa labarun da aka shirya a wannan rana , Mr. Mottaki ya ce , idan kasar Amurka ta yarda da shawarwarin kai-tsaye, to , a cikin shawarwari na sabon karon da za a yi nan gaba kadan , bangarori biyu za su tattauna wasu matsalolin da suke jawo hankulan mutanen duniya . Ya ce , yin shawarwarin irin wannan yana da muhimmanci sosai , kuma zai kawo babban tasiri mai kyau ga warwar matsalar nukiliyar kasar Iran .

Masu binciken al'amuran duniya suna ganin cewa , kasar Amurka ba za ta mai da hankali sosai ba kan wasikar shugaban kasar Iran . Mai yiwuwa ne Amerikawa suna ganin cewa , wannan wasikar katanga ce da kasar Iran ta sa a kan hanya wadda kasashen Yamma za su dauki mataki a Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya .

To, jama'a masu sauraronmu , shirin "Duniya ina labari " da za mu iya kawo muku ke nan a yau . Ado ne ya fassara wannan bayanin . Malam Lawal Mamuda ce ya karanto muku . Da haka muke muku sallama tare da fatan alheri .(Ado )