Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-08-28 15:56:55    
Kasar Massar ta yi kira da warware matsalar nukiliya ta kasar Iran ta hanyar yin shawarwari

cri

A ran 27 ga wata a birnin Alkahira, babban birnin kasar Massar, ministan harkokin waje na kasar Massar Ahmed Abulgheit ya yi kira ga bangarori daban daban da su warware matsalar nukiliya ta kasar Iran ta hanyar yin shawarwari.

Mr Abulgheit ya yi wannan bayani ne bayan da ya gana da mataimakin ministan harkokin waje na kasar iran Mohamed Reza Baqiri, wanda yake ziyarar aiki a kasar Massar. Ya ce, game da matsalar nukiliya ta kasar Iran, tilas ne Iran da kasashe 6 da suka gabatar da shirin kuduri su yi shawarwari da juna domin samun wata hanya da dukkan bangarorin su gamsu da ita.

Mr Baqiri ya ce, makasudin ziyararsa shi ne gaya wa kasashen Larabawa amsa da kasar Iran ta bayar ga shirin da kasashe 6 suka gabatar. Yana ganin cewa, an ce watakila kasashen yamma za su sanya takunkumi a kan kasar Iran, wannan ya zama ra'ayin kafofin watsa labaru kawai, ba ra'ayin da gwamnatoci suka bayar a hukunce ba.(Danladi)