Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-08-25 15:35:19    
Kasar Jamus ta nuna rashin jin dadi ga amsar da Iran ta bayar game da shirin kasashe shida

cri

An labarta, cewa jiya Alhamis, madam Angela Merkel firaministar kasar Jamus ta nuna rashin jin dadi ga amsar da gwamnatin Iran ta bayar game da shirin kasashe 6 dangane da maganar nukiliyar Iran. A sa'I daya kuma kasar Amurka ta kalubalanci Iran da ta yi zaben gaskiya ga kudurin da kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya tsaida na neman Iran da ta dakatar da shirinta na inganta sinadarin Uranium cikiin gajeren lokaci kafin karshen wannan wata.

A wannan rana, Madam Merkel ta furta, cewa a cikin amsar da Iran ta bayar, ba ta ce za ta dakatar da shirinta na inganta sinadarin Uranium cikin gajeren lokaci da kuma sake yin shawarwari ba. Wajibi ne ta kara wannan muhimmiyar magana.

Daga nata bangaren, gwamnatin Amurka ta sake nanata, cewa idan Iran ba ta aiwatar da kudurin kwamitin sulhu a ran 31 ga watan Agusta ba, to kasar Amurka za ta garkama wa Iran takunkumi ta kwamitin sulhun.

A wata sabuwa kuma, an ce, yau Jumma'a, ministan tsaro na kasar Rasha Mr. Sergey Ivanov ya fadi, cewa yanzu lokaci bai yi ba don tattauna batun garkama wa Iran takunkumi saboda batun ba shi da kan gado.

Jiya, gwamnatin Iran ta ce, a shirye take don fuskantar kowace irin abun da zai auku game da maganar nukiliya ta Iran. ( Sani Wang )