Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-08-24 18:20:56    
Kasar Iran ta riga ta shirya sosai a kan ko wane irin matakai da za a dauka

cri

A ran 24 ga wata, kakakin gwamnatin kasar Iran Gholam Hossein Elham ya bayyana cewa, kasar Iran ta riga ta shirya sosai a kan ko wane irin matakai da za a dauka a kan matsalar nukiliya.

Mr Elham ya ce, kasar Iran tana jiran kasashen Rasha da Sin da Ingila da Faransa da Jamus da Amurka su mayar da martani mai adalci ga amsa da kasar Iran ta bayar a rubuce a kan shirin kuduri da kasashe 6 suka gabatar. Amma a sa'i daya, ya karfafa cewa, kasar Iran za ta bi dokokin duniya da abin ya shafa, kuma ta yi imani cewa, za a iya warware matsalar nukiliyarta ta hanyar yin shawarwari bisa manyan tsare tsare na dokokin duniya.

Mr Elham ya ci gaba da cewa, kasar Iran ta riga ta ba da amsa ga kasashe 6 ta hanyar diplomasiyya, amma yanzu lokaci bai yi ba da za ta bayyana wannan amsa ga kafofin watsa labaru, domin wannan bai dace da manufofin da abin ya shafa ba.(Danladi)