Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-08-24 11:05:29    
Firayin ministan kasar Lebanon ya yi kira ga kasashen duniya da su ba da taimako kan ayyukan sake raya kasar

cri
Ran 23 ga wata, Fuad Siniora, firayin ministan kasar Lebanon ya yi kira ga kasashen Larabawa, da sauran kasashe kawaye da su shiga ayyukan sake raya kasar Lebanon bayan yaki.

A wannan rana a gun wani taron manema labaru, Mr. Siniora ya ce, sojojin Isra'ila sun kai farmaki kan kasar Lebanon daga sararin samaniya, sakamakon haka mutane da yawa sun ji rauni da mutu, da kuma hasarar dukiyoyi, wannan ya gurgunta tattalin arzikin kasar sosai, ayyukan sake rayar kasar Lebanon yana bukatar taimakon kudi da yawa. Bayan haka kuma ya bayyana cewa, yanzu sojojin gwamnatin Lebanon suna yin hadin kai da sojojin wucin gadi na M.D.D. da ke Lebanon a yankin da ke kudancin kasar, domin kara girke sojojin M.D.D..

A wannan rana, Tzipi Livni, ministan harkokin waje ta kasar Isra'ila, wadda ke yin ziyara a kasar Faransa ta kirayi a girka sojojin M.D.D. da ke Lebanon da sauri, domin tabbatar da zaman karko a shiyyar, a sa'i daya kuma, ya kamata M.D.D. ta tabbatar da wa'adin aikin sojojinta, da kuma nauyinsu.

A wannan rana a Beirut, Dora Bakoyannis, ministan harkokin waje ta kasar Greece, wadda ke yin ziyara a kasar Lebanon ta sanar da cewa, kasar Greece za ta aika da sojoji domin shiga sojojin wucin gadi na M.D.D.. Kasashen Sweden, da Denmark, da Norway, da kuma sauran kasashe su ma sun bayyana cewa, suna son ba da taimako kan harkar tsagaita bude wuta a Lebanon.

M.D.D. ta sanar da cewa, a 'yan kwanaki masu zuwa, Kofi Annan, babban sakataren M.D.D. zai kai ziyara ga yankin Gabas ta tsakiya, domin karfafa yin kira ga bangarori daban daban da su aiwatar da kuduri na nambar 1701 na kwamitin sulhu. (Bilkisu)