Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-08-22 15:49:14    
Iran za ta cigaba da gudana da shirita na nukiliya, kungiyar EU za ta rika tuntubar Iran

cri

Ran 21 ga wata, Ali Khamenei shugaban koli na kasar Iran ya ce, kasar Iran za ta cigaba da gudana da shirinta ta nukiliya. A wannan rana kuma Javier Solana wakili mai kula da harkokin waje da manufofin tsaro ya nuna cewa, kungiyar gammayar kasashen Turai (EU) za ta rika "cigaba da tuntubar" Iran.

Khamenei ya yi jawabi ta gidan TV cewa, kasar Iran ta riga ta tsai da shirin yin amfani da makamashin nukiliya, kuma za ta tafiyar da wannan shiri tare da cikakkiyar azama. Mr. Mohammad Sa'eedi mataimakin shugaban kungiyar makamashin nukiliyar kasar Iran ya nuna cewa, bisa halin da ake ciki yanzu ba zai yiyu kasar Iran ta daina yin binciken nukiliya, kasar Iran za ta fara aiki kan wata babbar na'ura mai inganta ruwa.

Javier Solana ya yi shawarwari tare da Larijani wakili na farko na shawarwarin nukiliya ta waya kan wannan batun. Ya ce, dukansu za su cigaba da tuntubar juna.

Bisa labarin da muka samu, wani jami'in hukumar makamashin nukiliyar kasashen duniya ya ce, kasar Iran ta riga ta ki masu bincike na hukumar su bincike na'urar nukiliya da ke birnin Natanz.