Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-08-22 10:41:22    
Shugaba Bush na kasar Amurka ya yi kira ga kasashen duniya da su aike da sojoji zuwa kasar Lebanon

cri

Wakilin Rediyon kasar Sin ya ruwaito mana labari cewa , A ran 21 ga watan nan a gun taron manema labaru da aka shirya a Fadar gwamnatin Amurka , shugaba Bush na kasar Amurka ya yi kira ga kasashen duniya da su aike da sojoji zuwa kasar Lebanon don shiga rundumar sojojin Majalisar Dinkin Duniya . Sa'an nan kuma ya bayyana cewa , idan sojojin kasar Amurka su janye jiki daga kasar Iraq , to , zai zama wani kuskure ne .

Mr. Bush ya ce , dole ne kasashen duniya su tsai da kudurin wace kasa za ta shugabanci sojojin MDD dake kasar Lebanon . .

Mr. Bush ya kuma sanar da cewa kasar Amurka za ta samar da kudin taimako dala miliyan 230 ga kasar Lebanon don farfado da kasar bayan yakin. Mr. Bush ya kuma bayyana cewa , idan sojojin kasar Amurka su janye jiki daga kasar Iraq , to , Iraq za ta shiga cikin bala'in . Idan gwamnatin kasar Iraq ta ci tura , to , Iraq za ta zama wurin 'yan ta'adda .. (Ado)