Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-08-21 11:28:57    
Sojojin tsaron kasar Isra'ila sun kama babban sakataren kwamitin kafa dokoki na Falestinu

cri
Ran 20 ga wata, wani jami'in Falestinu ya shaida cewa, a wannan rana a shiyyar da ke yammancin bakin kogin Jordan, sojojin tsaron kasar Isra'ila sun kama Mahmoud al-Ramahi, babban sakataren kwamitin kafa dokoki na Falestinu.

Wadanda aka yi wannan lamari a kan idanunsu sun ce, sojojin tsaron kasar Isra'ila sun kewaya gidan Mahmoud al-Ramahi da ke garin Birah da ke kusa da birnin Ram Allah a yammancin bakin kogin Jordan, kuma sun kame shi.

Tun bayan da 'yan dakarun Falestinu suka kama wani soja na Isra'ila a ran 25 ga watan Yuni a shiyyar da ke kusa da Gaza, bangaren Isra'ila ya kara dauka matakan murkushe kungiyar Hamas, da kuma sauran kungiyoyin dakarun 'yan tawaye na Falestinu, kuma sun kama ministocin gwamnatin wucin gadi ta Falestinu, da muhimman jami'an Hamas na kwamitin kafa dokoki daya bayan daya. (Bilkisu)