Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-08-20 21:14:56    
Kasar Iran ta ce, ya zuwa yanzu ba ta tsara jadawalin dakatar da aikin sarrafa sinadarin Uranium ba tukuna

cri
Yau ran 20 ga wata, Hamid-reza Asefi, kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Iran ya bayyana a birnin Tehran cewa, ya zuwa yanzu, kasar Iran ba ta tsara jadawalin dakatar da sarrafa sinadarin Uranium ba tukuna. A wannan rana kuma kasar ta harba wani makami mai linzami bisa gwaji.

A gun taron manema labaru da aka saba yi a wannan rana, Asefi ya ce, abin da ake nufi da dakatar da aikin sarrafa sinadarin Uranium shi ne komawa baya, amma yanzu kasar Iran ba ta tsara jadawalin yin haka ba. Ya kuma jaddada cewa, ya zuwa yanzu, kasar Iran tana ganin cewa, wajibi ne, a daidaita batun nukiliyarta ta hanyar shawarwari, amma bai kamata a gabatar da babban sharadi ga shawarwarin da za a yi ba.

Da ya tabo magana a kan shirin daidaita batun nukiliyar kasar Iran da Rasha da Amurka da Sin da Birtaniya da Faransa da kuma Jamus suka gabatar a farkon watan Yuni da ya wuce, sai Asefi ya ce, kasar Iran ta riga ta shiga lokacin karshe da take yin bincike a kan wannan shiri. Ganin yadda shirin ya shafi batun nan a fannoni da yawa, kasar Iran za ta ba da amsa ga wannan shiri ma a fannoni da yawa. (Halilu)