Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-08-20 18:15:59    
Kasar Iran ta harbi wani makami mai linzami na gajerren zango

cri
Bisa labarin da muka samu daga gidan talibijin na kasar Iran, an ce, a ran 20 ga wata, kasar Iran ta harbi wani makami mai linzami na gajerren zango wanda ake kiransa "Saegheh".

Kuma an bayyana cewa, bangaren sojojin Iran ya harbi wannan makami mai linzami ne a shiyyar hamada ta Kashan da ke da nisan kilomita 250 tsakaninta da birnin Teheran, babban birnin kasar Iran.

A ran 19 ga wata, bangaren sojojin Iran ya fara gagarumin atisaye na makwani biyar na sojojin kasa da na jiragen sama da kuma na jiragen ruwa a duk fadin kasar wanda shi ne karo na biyu da aka yi a cikin shekarar da muke ciki, kuma nufinsa shi ne gwaje sabbin dabarun yaki iri daban daban da kuma jarraba wasu sabbin makamai.(Kande Gao)