Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-08-16 18:46:28    
An buga littattafai na rukunin farko da aka bari a da a wurin Dunhuang

cri

Kwanan baya, an gabatar da littattafai 30 na da na Dunhuang wadanda gidan ajiye littattai na kasar Sin ya buga ta hanyar daukar hotuna ga jama'a. Wannan ne kashi na farko da aka buga littattafai na da na Dunhuang bisa babban mataki, wannan ya bayyana shahararren ci gaba da masu nazari na kasar Sin suka samu wajen gyara littattafan da aka bari da kiyaye su da yi nazarinsu.

A shekarar 1900, a wurin Dunhuang na lardin Gansu da ke arewa maso yammancin kasar Sin, an gano littattafai da yawa na zamanin da wato daga karni na 5 zuwa karni na 11, sai an nada sunayen wadannan littattafai cewa, littattafan Dunhuang da aka bari. Ta hanyar yin amfani da rubuce-rubucen harshen Han da Tufan da Fan da dai sauransu ne suka rubuta abubuwa dangane da addinai da yanayin kasa da al'adun 'Yan Adam da halayen musamman da aka yi a tarihi da dai sauransu, su ne takardun da aka adana masu daraja sosai ga yin bincike kan kasar Sin ta zamanin aru aru da zaman rayuwar da ake yi a gabashin Asiya. A cikin shekaru 20 da suka wuce, littattafan Dunhuang da aka bari masu yawa sun fita daga kasar Sin, yanzu a duk duniya, da akwai kasashe da jihohi da yawansu ya kai 40 ko fiye da suka ajiye littattafan Dunhuang da aka bari, daga cikinsu ,kasashen Britaniya da Faransa da Rasha da Japan suna da irin littatafai da yawa.

Gidan ajiye littattafai na kasar Sin shi ne inda aka ajiye littattafan Dunhuang mafiya yawa, gidan nan yana da irin littattafai da yawansu ya kai dubu 16 ko fiye wanda ya kai kashi daya cikin kashi uku na yawan irin littattafan da aka tanada. Saboda shekaru da yawa da suka wuce, littattafan nan sun lalace sosai da sosai. Daga shekaru 80 na kanirn da ya shige, gidan ajiye littattafai na kasar Sin ya soma gyara su. Yanzu, an riga an sami babban sakamako wajen gyara irin littattafai, bisa tushen nan ne, gidan ajiye littattafai na kasar Sin ya tsai da kudurin daukar hutunansu don sake buga su, yawansu ya kai 150, an kimanta cewa, za a kammala aikin nan a karshen shekarar 2007. Mataimakin shugaban gidan nan Chen Li ya gaya wa manema labaru cewa, sake buga dukan irin wadannan littattafai buri ne na masu yin bincike kan ilmin Dunhuang na gida da na waje. Ya bayyana cewa, ya kamata a kiyaye kayayyakin al'adu na tarihi, a sa'I daya kuma a yada su, wannan ne wani fanni mai muhimmanci wajen yada al'adun al'umma.

Mr Chen Li ya ci gaba da cewa, daga shekaru 30 na karnin da ya wuce, kasar Sin ta kafa hukumomin musamman na tattarawa da kiyaye littattafan Dunhuang da aka bari, a shekaru 80 na karnin, an soma gyara su don sake buga su.

Malam Zhang Zhiqing shi ne mataimakin direkta na sashen ajiye littattafai na musamman na gidan nan kuma mashahurin kwararre ne na kiyaye littattafai na shekaru aru aru. Ya bayyana cewa, ta hanyoyin musamman na gargajiya da yawa ne za a iya gyara irin wadannan littattafai. Mr Zhang ya bayyana cewa, yadda za a buga littattafan Dunhuang da za a iya duddubawa sosai da sosai tare da cikakkun abubuwan da suke tanada, dawainiya ce gare mu. Bisa halin nan da muke ciki, sai muka daukar hotunansu don buga su, bayan gwajin da muka yi, sai muka sami sakamako mai kyau. Wani malamin da ke aiki a sashen musamman na gidan ajiye littattafai na kasar Sin Lin Shitian ya bayyana cewa, yanzu, zamani ne na yin amfani da lisafi, amma wajen fannin nan, dayake an sami bambancin tunani bisa bambancin al'adu da bambancin fasahohi. Ta hanyar hadin guiwa a tsakanin kasa da kasa ne , mu iya yin amfani da wasu fasahohin da aka samu daga kasashen ketare da shigar da fasahohin zamani da hanyoyin kula da harkokin ayyuka kai tsaye. Ya kuma ce,buga littattafan Dunhuang na da ya ba da sauki sosai ga yin nazarin ilmin Dunhuang. (Halima)