Ran 15 ga wata, a birnin Ardebil da ke arewa maso yammacin kasar Iran, shugaban kasar Iran Mr. Mahmoud Ahmadinejad ya bayyana cewa, kasar Iran ba za ta amince da kuduri mai lamba 1696 da kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya zartas da shi a kan batun nukiliya na kasar Iran a kwanan baya ba.
A gun wani taron jama'a da aka yi a ran nan, Mr. Ahmadinejad ya yi bayanin cewa, kada kwamitin sulhu ya tilasta wa kasar Iran ta amince da wannan kuduri, wajibi ne ya gane cewa, kasar Iran ba za ta yi rangwame saboda barazanar da aka yi mata ba.
Ban da wannan kuma, Mr. Ahmadinejad ya ce, a kwanan baya, ya amsa wayar tarho daga babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Mr. Kofi Annan, inda ya bukaci kasar Iran da ta amsa shirin kasashe 6 da kasashen duniya suka bayar. Ya gaya wa Mr. Annan cewa, kasar Iran tana son warware matsala ta hanyar yin tattaunawa, amma kudurin da kwamitin sulhu ya zartas da shi ya sa kasar Iran ta canza shawara.(Tasallah)
|