A ran 11 ga wata da alfijir, jiragen sama na sojojin Isra'ila sun ci gaba da jefa boma bomai a arewacin kasar Lebanon da kudancin birnin birnin Beirut, babban birnin kasar Lebanon. Wannan ya riga yi yi sanadiyyar mutuwar mutane a kalla 11 a yayin da mutane 9 suka ji rauni.
Bisa labarin da muka samu, an ce, a ran 10 ga wata da dare, kasar Rasha ta riga ta bayar da wani shirin kuduri ga mambobin kwamitin sulhu 15 na MDD, inda ta yi kira ga bangarorin Lebanon da Isra'ila da su tsagaita bude wuta cikin awoyi 72 nan da nan, domin kungiyoyin ba da agaji na duniya su ba da taimakon jin kai.
Bisa labarin da kafofin watsa labaru na kasar Isra'ila suka bayar, an ce, zaunannen wakilin kasar Isra'ila a MDD Dan Gillerman ya riga ya ki yarda da wannan shirin kuduri da kasar Rasha ta gabatar.(Danladi)
|