Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-08-11 15:36:15    
Gagarumin bikin nishadi na marabtar zuwan taro wasannin Olympics a nan Beijing

cri

Jama'a, kuna sanin cewa, shirya taron wasannin motsa jiki na Olympics, ba takara kawai da nagartattun 'yan wasa na kasashe daban daban sukan yi ba ; Akan shirya irin wannan taron wasanni ne domin yada wasannin motsa jiki, ta yadda mutane mafi yawa za su halarta tare da samun lafiyar jiki da kuma morewa. Muhimmin makasudin bikin al'adu na 4 na Olympics da aka kammala kwanakin baya ba da dadewa ba a nan Beijing, shi ne domin yada hasashen Olympics a kan cewa dukkan mutane su shiga cikin wasannin motsa jiki.

A kwanakin baya ba da jimawa ba, hadaddiyar kungiyar sada zumunta tare da kasashen ketare ta jama'ar birnin Beijing da kuma sauran hukumomin da abun ya shafa sun gudanar da wata gagarumin nishadi na wasannin motsa jiki da al'adun jama'a na kasa da kasa na Beijing wato yin wasannin motsa jiki a safiya a kasar Sin dake shirin shirya taron wasannin Olympics. Lallai wannan harka ta jawo hankulan dimbin wakilan mazauna birnin, da jakadun kasashen ketare dake nan kasar Sin da kuma aminai daga kasashe daban daban wadanda suka zo nan musamman domin halartar harkar nan.

A cikin wadannan aminai baki, akwai wassu ' yan kungiyar sada zumunta ta wasan dambe na gargajiya na kasar Sin wato Taijiquan ta kasar Japan, wadanda suka zo nan musamman domin halartar bikin nishadin da aka yi a nan Beijing. Ko da yake ya kasance da bambancin al'adu tsakanin kasashen Japan da Sin, amma wadannan aminai Japanawa dukkansu suna sha'awar irin wannan tsohon wasan gargajiya wato Taijiquan.

Madam Taeri Hitai mai shekaru 27 da haihuwa, wata ma'aikaciya ce ta wani kamfani a Tokyo na kasar Japan. Shekaru uku da rabi ke nan da ta soma yin wasan dambe na gargajiya na kasar Sin wato Taijiquan. Da ta iso nan Beijing a wannan gami, sai ta yi mamaki da ganin yadda ake yin mashashan aikin gina manyan ayyuka da yawa. Madam Hitai tana began taron wasannin motsa jiki na Olympics da za a yi a nan Beijing a shekarar 2008. Ta furta, cewa:

'Japanawa dukkansu suna begen taron wasannin Olympics na Beijing. Kasar Sin ita makwabtaciya ce ta Japan, kuma akwai bambancin lokaci na awa daya kawai tsakanin kasashen biyu. Don haka, za mu iya kallon wasanni masu ban sha'awa a kowace rana'.

Aminai baki kamar Madam Hitai masu kaunar al'adun kasar Sin, wadanda suka zo nan Beijing a wannan gami domin halartar harkar nishadi, wannan dai wani halin musamman ne na harkar nan. Mr. Li Jie, daraktan cibiyar ba da jagoranci ga wasannin motsa jiki na jama'a ta babbar hukumar wasannin motsa jiki ta kasar Sin ya fadi, cewa:

' Aminai baki sun zo nan Beijing don halartar bikin al'adu da aka gudanar da shi a wannan gami. Wannan dai ya fadakar da mu a kan cewa yin wasannin motsa jiki tare da halartar dukan jama'a domin marabtar zuwan taron wasannin Olympics, ba ma kawai ya kago sharadi ga Sinawa ba, har ma ga dukkan mutane dake yin aiki a nan kasar Sin, da ma'aikatan ofisoshin jakadun ketare dake nan kasar da kuma ' yan kasuwa baki. Wannan abu ya zama tamkar taimako ne da taron wasannin Olympics da za mu shirya ya bai wa jama'ar kasashe daban daban.

A gun bikin nishadin, wassu tsofaffi sun nuna wasan dambe na gargajiya na kasar Sin wato Taijiquan mai ban sha'awa. Kaka Wang yana daya daga cikinsu. Unguwar Kaka Wang, wuri ne da aka gina kauyen 'yan wasa na Olympics a can. Ya yi farin ciki matuka da fadin, cewa:

' Da sahihiyar zuciya ne nake begen taron wasannin Olympics na Beijing a shekarar 2008 zai zama wani gagarumin taron wasanni mafi kyau na duniya.'( Sani Wang )