Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-08-10 15:19:27    
Hezbollah ta yarda da gwamnatin kasar Lebanon ta shimfida sojojinta a kudancin kasar

cri

Ran 9 ga wata, Mr. Sheikh Hassan Nasrallah babban sakataren jam'iyyar Hezbollah ya yi jawabin TV cewa, bayan an tsakaita bude wuta kuma kasar Isra'ila ta janye jiki daga kasar Lebanon, jam'iyyar Hezbollah za ta goyon baya kudurin shimfida sojojin gwamnatin kasar Lebanon da gwmantin ta yi.

Amma a sa'i daya kuma Sheikh Hassan Nasrallah ya nuna danuwa ga sojojin gwamnaitin da za a shimfida a kudancin. Ban da haka kuma, Nasrallah ya zargi shirin kudurin da kasashen Amurka da Faransa suka gabata a kwanaki baya rashin adalci. A wannan rana kuma Fawzi Salukh ministan harkokin waje na kasar Lebanon ya yi kira kwamitin sulhu na MDD ya yarda da shawarwrin da Lebanon ta gabata, wato gyara shirin kudurin da kasar Amurka ta gabata.

Shugaba Chirac na kasar Faransa ya ce, kasar Faransa ta riga ta gyara shirin kuduri, idan kasashen biyu ba za su sami ra'ayi iri daya, kasar Faransa za ta gabatar da kuduri ga kwamitin shulhu ita kadai. Mr. Tony Snow kakakin ofishin shugaban kasar Amurka ya ce, kasar Amurka tana yin kokarinta don kauce wa ra'ayoyi masu banbanci da ke tsakaninta da saruran kasashe. Bisa lahin da ake ciki yanzu, ba a iya tabbatar da yaushe kwamitin shulhu zai kada kuri'a kan wannan shiri.