
A ran 7 ga wata, Mr. Effah Apenteng shugaban kwamitin sulhu na wannan wata kuma zaunannen wakilin kasar Ghana da ke MDD ya ce, shugaban kungiyar gamayyar kasashen Larabawa (LAS) da ministocin harkokin waje na kasashen Larabawa biyu za su kai ziyara ga kwamitin sulhu a watan gobe, a lokacin, kwamitin sulhu na MDD zai saurari ra'ayoyinsu wajen warware rikicin da ake yi a tsakanin Lebanon da Isra'ila. Bayan haka, za a iya tabbatar da shirin kudurin da kasashen Faransa da Amurka suka gabatar.
Zaunannen wakilin kasar Fasanra a MDD Mr Sabliere ya ce, kasar Faransa za ta gyara shirin kudurin domin kula da ra'ayoyin sauran mambobin kwamitin sulhu na MDD.
Zaunannen wakilan kasar Amurka da ke MDD John Bolton ya ce, kafin kwamitin sulhu ya zartas da kudurin, zai saurari ra'ayin kasashen Larabawa, kasar Amurka kuma za ta saurari ra'ayoyin sauran membobin kwamitin sulhu, bayan haka za ta yi la'akari da cewa ko za ta yi gyara a kan shirin ko a'a.
A ran 8 ga wata, zaunannen wakilin kasar Rasha da ke MDD Vitaly Churkin ya bayyana cewa, kasar Rasha ta ki yarda da zartas da shirin da Amurka da Fasansa suka gabatar, sabo da wannan shiri bai dace da moriyar Lebanon ba, wannan shiri zai hana a warware ricikin da ake yi a tsakanin Lebanon da Isra'ila cikin sauri.(Danladi)
|