Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-08-08 10:35:40    
Kasashen Larabawa sun goyi bayan shirin daidaita rikicin da ke Isra'ila da Lebanon da gwamnatin Lebanon ta gabatar

cri

A ran 7 ga wata a birnin Beirut na kasar Lebanon, an yi taron ministocin kungiyar tarayyar kasashen Larabawa cikin gaggawa, inda aka jaddada cewa, suna goyon bayan ka'idoji 7 da gwamnatin kasar Lebanon ta gabatar wajen kawo karshen rikicin da ake yi a tsakanin Isra'ila da Lebanon.

Sannan kuma, a gun taron, an tsai da kudurin cewa, za a aika da wata kungiyar wakila wadda ke karkashin jagorancin babban sakatare Amr Moussa na Tarayyar kasashen Larabawa zuwa birnin New York domin sanar wa babban sakatare Kofi Annan da zaunannun wakilan kasashen kwamitin sulhu na M.D.D. matsayin da kasashen Larabawa suke dauka, kuma za su yi kokari wajen yin kwaskwarima kan shirin kuduri game da batun rikicin da ke tsakanin Isra'ila da Lebanon da za a tattauna shi a zauren kwamitin sulhu na M.D.D.

A wannan rana, ministan harkokin waje na kasar Faransa Philippe Douste Blazy ya bayyana cewa, gwamnatin kasar Faransa ta amince da cewa, za ta yi gyara kan shirin kudurin da kasar Faransa da kasar Amurka suka gabatar tare game da batun daidaita rikicin da ke tsakanin Isra'ila da Lebanon bisa bukatun da kasashen Larabawa da kasar Lebanon suke nema.

A waje daya kuma, shugaba George W. Bush na kasar Amurka ya bayyana cewa, kasar Amurka tana kokari tare da sauran kasashen duniya domin yunkurin daidaita rikicin da ke tsakanin Isra'ila da Lebanon a zauren M.D.D. da shimfida zaman lafiya mai dorewa a yankin.

Bugu da kari kuma, majalisar ministocin gwamnatin Lebanon ta tsai da kudurin cewa, idan Isra'ila ta janye sojojinta daga yankunan kudancin kasar Lebanon, kasar Lebanon za ta tanadi sojoji dubu 15 a yankunan. Sannan kuma, firayin minista Ehud Olmert na kasar Isra'ila ya bayyana a wannan rana cewa, ba za a kayyade dukkan matakan soja da sojojin Isra'ila za su dauka ba domin hana hare-haren rokokin da dakarun kungiyar Hezbollah za su harba a kan yankunan arewacin kasar Isra'ila. (Sanusi Chen)