Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-08-07 15:39:49    
Jiragen sama na sojojin Isra'ila sun kai farmaki kan shiyyar da ke kudancin kasar Lebanon, sakamakon haka fararen hula 11 suka rasa rayukansu

cri

Ran 7 ga wata, bangaren 'yan sanda na kasar Lebanon ya ce, a wannan rana da safe, jiragen sama na sojojin Isra'ila sun kai farmaki kan shiyyar da ke kudancin kasar Lebanon, sakamakon haka fararen hula 11 suka rasa rayukansu.

A wannan rana da safe, jiragen sama na sojojin Isra'ila sun kai farmaki kan shiyyar da ke kudancin birnin Sidon, wato wani muhimmin birni da ke kudancin kasar Lebanon, kuma sun ragargaza wani gini mai benaye 3, sakamakon haka muatne 7 sun mutu. Daga baya kuma, sojojin Isra'ila sun jefa boma-bomai daga sarari kan wani gida da ke shiyyar gabashin birnin Sidon, fararen hula 4 sun mutu a sakamakon haka.

A wannan rana kuma, jiragen sama na sojojin Isra'ila sin jefa boma bomai fiye da sau 10 kan wasu muhimman gine-gine da ke gabashin birnin Sidon, wannan kuma ya lalata wasu hanyoyin da ke tsakanin kasashen Lebanon da Sirya, amma ya zuwa yanzu ba a samu rahoto game da sunayen mutanen da suka jin rauni ko mutuwa. (Bilkisu)