Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-08-06 21:52:55    
Iran ta yi shelar ci gaba da kuma habaka aikinta na tace sinadarin uranium

cri
Wakilin Iran na farko a kan shawarwarin nukiliya, kuma sakataren babban kwamitin tsaron kasar, Ali Larijani ya bayyana a yau ranar 6 ga wata cewa, Iran za ta ci gaba da kuma habaka aikinta na tace sinadarin uranium, a maimakon daina shi.

A gun taron manema labaru da aka yi a ranar a birnin Teheran, babban birnin Iran, Mr.Larijani ya ce, kudurin da kwamitin sulhu ya zartas a karshen watan Yuli ba na halal ba, kuma ba zai kawo tasiri a kan kudurin Iran ba.

Mr.Larijani cewa ya yi, kudurin kwamitin sulhu ya saba wa shirin kasashe shida da gamayyar kasa da kasa suka gabatar a farkon watan Yuni, haka kuma ya musanta rawar da hukumar makamashin nukiliya ta duniya ke takawa. Ya kara da cewa, Iran ba ta karya ko wane alhakin da aka tanada a cikin yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya ba, MDD ba ta da hakkin neman Iran da ta daina ayyukan tace sinadarin uranium, sabo da haka, Iran za ta ki amince da kudurin.(Lubabatu Lei)