Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-08-04 21:55:49    
Kungiyar kasashen musulmi ta duniya ta la'anci aikace-aikacen hare haren da kasar Isra'ila take yi

cri

Ran 3 ga wata a Putrajaya, wato cibiyar hukuma ta kasar Malaysia, wasu kasashe mambobi na kungiyar kasashen musulmi sun shirya taro na gaggawa, bayan haka kuma sun bayar da wata sanarwa, inda suka la'anci hare haren da kasar Isra'ila ta ke yi wa kasar Lebanon.

Shugabanni, da ministocin kasashen waje, da kuma wakilan wadannan kasashe mambobi na kungiyar kasashen musulmi, kamar su Malaysia, da Indonesiya, da Iran, da Palestinu, da Lebanon, da kuma Sirya, da dai sauransu sun halarci wannan taron da aka shafe kwana 1 ana yinsa.

Taron ya bayar da wata sanarwa dangane da halin da kasar Lebanon ke ciki, inda aka cewa, hare haren da kasar Isra'ila ke yi wa kasar Lebanon ya shafi dukkan yankunan kasar Lebanon, da kuma yancin kanta. Sanarwar tana ganin cewa, ya kamata kasar Isra'ila ta dauke hakki kan sakamakon da aikace-aikacen kai hari ke kawowa. Bayan haka kuma, mahalarta taron sun bukacin a yi binciken kasa da kasa kan laifin yaki da kasar Isra'ila ke aiwata a kasar Lebanon.

A sa'i daya kuma, sanarwar ta karfafa yin kira ga kwamitin sulhu na M.D.D. da ya dauke nauyinsa na kiyaye zaman lafiya a duniya, da kuma daukar matakai domin tabbatar da tsagaita bude wuta nan da nan a dukan fannoni. Sanarwar ta ba da shawarar a girke sojojin kiyaye zaman lafiya na kasashen duniya da M.D.D. ta ba da cikakken ikon yi, kuma kasashen musulmi za su halarci a shiyyar bakin iyakar da ke tsakanin Lebanon da Isra'ila. Kasashen Malaysia, da Indonesiya, da kuma Brunei



Darussalam, da dai sauransu, dukansu sun yarda da aika da sojoji,domin halarcin aikace-aikacen kiyaye zaman lafiya.
Bayan haka kuma, mahalarta taron sun nuna goyon baya ga shawarwari 7 da gwamnatin kasar Lebanon ta gabatar a 'yan kwanakin da suka wuce dangane da kasashen Lebanon da Isra'ila su tsagaita bude wuta nan da nan a duka fannoni. Inda suka kunshi musayen sojoji da mutanen da ake tsare da su tsakanin kasashen, da sojojin Isra'ila sun janye jiki zuwa iyakar bakin kasa ta wucin gadi, da kuma sauran abubuwa.

Fawzi Salloukh, ministan harkokin waje na kasar Lebanon da ke hallatar taron ya bayyana cewa, kasar Lebanon za ta kiyaye yankuna da yancin kanta a cikin goyon bayan kasashen duniya. A sa'i daya kuma ya bukacin kafa wani kwamitin dokoki na duniya, domin binciken mugun aiki da sojojin Isra'i'a suka yi wajen kai farmaki kan shiyyar da ke kudancin kasar Lebanon, wanda ya haddasa mutuwar fararen fula, kuma a mayar da 'yan gudun hijira na kasar Lebanon da su sake koma gidajensu da wuri. Bayan taron, Mr. Sallokh ya gaya wa maneman labaru cewa, sanarwar za ta iya ingiza kwamitin sulhu da ya tsaida kuduri, domin tabbatar da tsagaita bude wuta nan da nan a dukan fannoni, kuma ba tare da sharadi ba a tsakanin kasashen Lebanon da Isra'ila.

Ran 3 ga wata, Abdullah Ahmad Badawi, firayin ministan kasar Malaysiya, wato kasar shugaba ta kungiyar taron musulunci a yanzu ya gaya wa maneman labaru cewa, zai rubuta wasiki ga shugaba Bush na kasar Amurka a ran 4 ga wata, inda zai yi kira ga kasar Amurka da ta ingiza tabbatar da tsagaita bude wuta a tsakanin Lebanon da Isra'ila. A sa'i daya kuma, ya nuna cewa, ban da kasashen Amurka da Ingila, sauran kasashe masu kujerar din din din a kwamitin sulhu na M.D.D., da Kofi Annan, babban sakataren M.D.D. dukansu sun yarda da bukacin bangarorin Lebanon da Isra'ila su tsagaita bude wuta nan da nan. Amma, ra'ayin kasashen Amurka da Ingila ya sa kasar Isra'ila ta kara tsananta kai farmakin soja. Mr. Badawi ya bayyana cewa, wannan ne abin bakin ciki. (Bilkisu)