Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-08-04 11:08:28    
Kasar Iran tana nazari a kan shirin da kasashe 6 suka gabatar da shi

cri

A ran 2 ga wata a birnin Tokyo, mataimakin shugaban kasar Iran Isfandiar Rahim Mashaee, wanke yake ziyarar aiki a kasar Japan, ya bayyana ceaw, ko da yake kwamitin sulhu na MDD ya zartas da sabon kuduri dangane da kasar Iran, amma kasar Iran tana nazari a kan shirin da kasashe 6 suka gabatar da shi.

An ce, a gun ganawar da ke tsakanin Mr Mashaee da ministan harkokin waje na kasar Japan Aso Taro, Mr Mashaee ya ce, kasar Iran tana nazari a kan shirin da kasashe 6 suka gabatar, amma kwamitin sulhu bai kula da haka ba, ya zartas da sabon kuduri game da kasar Iran, wannan ya bayyana cewa, kasashen yamma suna son warware matsalar nukiliya ta kasar Iran ta hanyar yi wa kasar Iran matsin lamba a maimakon yin shawarwari, kuma suna son cire halalcin ikon Iran.

Mr Mashaee ya sake nanata cewa, kasar Iran ba za ta sadaukar da ikonta na yin amfani da makamashin nukiliya cikin lumana ba, wannan shi ne ra'ayin da dukkan jama'ar kasar Iran suka tsaya a kai.(Danladi)