A ran 1 ga wata, a birnin Teheran, babban birnin kasar Iran, Kazem Jalali, kakakin kwamitin harkokin waje na majalisar dokoki ta kasar Iran ya bayyana cewa, Iran ba za ta iya karbar kuduri mai lamba 1696 da kwamitin sulhu na MDD ya zartas kan batun nukiliya nata ba.
Yayin da yake zantawa da manema labarai na wurin, Jalali ya ce, kudurin ya canja halin da ake ciki yanzu wajen warware batun nukiliya na Iran, idan an ci gaba da yin haka, to ba za a kawo alheri ga ko wane bangare ba.(Kande Gao)
|