Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-08-01 20:14:56    
Yin barci cikin awoyi 7 a ko wace rana ya fi amfana wa lafiyar mutate

cri

Yanzu ga shirinmu na kimiyya da ilmi da kuma kiwon lafiya. Da farko za mu gabatar muku da wani labari dangane da kiwon lafiya , sa'an nan kuma za mu gabatar muku da wani bayanin da ke da lakabi haka 'Kasar Sin ta dora muhimmanci kan ba da ilmin jima'i tsakanin matasa'.

Yanzu za mu soma gabatar muku da labarin da muka shirya muku.

Ko wace ya sani cewa, rashin barci ya kawo wa lafiyar mutane illa. Amma yin barci cikin dogon lokaci bai amfana wa lafiyar mutane ba. Masana masu ilmin likitanci sun nuna cewa, yin barci cikin awoyi 7 a ko wace rana ya fi amfana wa lafiya.

Shehun malami Li Shunwei, zaunannen wakilin sashen ilmin kwakwalwa na hadadiyyar kungiyar ilmin likitanci ta kasar Sin ya bayyana cewa, lokacin barci wani muhimmin abin bara ne wajen tabbatar da rashin barci. Idan wani mutane bai iya yin barci cikin awoyi 6 a duk rana gaba daya ba, to, likitoci sun tabbatar da cewa, wannan mutum ya kamu da ciwon rashin barci.

Yin barci cikin dan lokacin kadan zai kawo wa lafiyar mutane illa. Nazarin da aka yi ya nuna cewa, masu fama da rashin barci da yawansu ya kai kashi 80 zuwa 90 cikin dari sun fama da sauran ciwace-ciwace, wadanda ke kunshe da ciwon zuciya da hawan jini da sauran ciwace-ciwace masu tsanani.

Mr. Li ya tsamo sakamakon nazarin da abin ya shafa ya yi nuni da cewa, yin barci cikin dogon lokaci ko kuma cikin dan lokaci kadan sun haddasa ciwon sukari da ciwon zuciya, har ma sun kara wa mutane barazanar mutuwa, yin barci cikin awoyi 7 a ko wace rana ya iya rage wa masu fama da ciwon sukari da ciwon zuciya barazanar mutuwa.

Masanan da abin ya shafa sun nuna cewa, a galibi dai akwai manyan dalilai 3 da suka ba da tasiri kan barci su ne ciwace-ciwace da halin mutane da kuma matsin lambar aiki da dangantakar da ke tsakanin mutane. Ga misali, ciwo ya kan ba da tasiri kan barci, haka kuma, jarrabawa ta kan ta da hankalin dalibai.

Wasu kwararru masu ilmin abinci masu gina jiki sun ba da shawarar cewa, abinci masu yawa sun ba mutane taimako a fannin yin barci. Madara mai zafi da ke kunshe da zuma da dabino da zuma da tuffa da dai sauransu dukansu sun ba da taimako wajen yin barci, zaben abinci yadda ya kamata ya iya daga ingancin barci.

A sa'i daya kuma, Mr. Li ya bayyana cewa, an sami wadannan sakamakon nazari ne bayan da aka yi nazari kan yawancin mutane, ba a iya kawar da cewa, ko da yake su kan yi barci cikin awoyi 4 zuwa 5 a ko wace rana, ko kuma cikin awoyi fiye da 10, wasu mutane suna da lafiya ba.