Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-07-31 14:54:44    
Kwamitin sulhu na MDD ya nuna matukar mamaki ga hare-hare da sojojin Isra'ila suka kai a kan kauyen kudancin Lebanon

cri
Taron gaggawa da kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya ya shirya a ran 30 ga wata, gaba daya ya zartas da sanarwar shugabansa, inda ya nuna matukar mamaki da bakin ciki ga harin bama-bomai da sojojin sama na kasar Isra'ila suka kai a kan kauyen Qana a kudancin kasar Lebanon da babbar hasarar rayukan mutane da jima musu raunuka, kuma ya yi kira da a daina nuna karfin soja.

Sanarwar ta ce, kwamitin sulhu ya nuna babbar ta'aziyya ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu da jama'ar kasar Lebanon, kuma ya nuna matukar bakin ciki ga mutuwar jama'a wadanda ba su ci ba su sha ba. Haka zalika ya nemi Kofi Annan, sakatare-janar na majalisar dinkin duniya da ya gabatar da wani rahoto a kan wannan al'amari mai bakanta rai nan da wani mako. Sanarwar ta kara da cewa, kwamitin sulhu yana mai da hankali ga tabarbarewar halin da ake ciki a kasar dangane da jin kai, ya yi kira da a daina nuna karfin soja, kuma ya karfafa magana a kan muhimmancin tsagaita bude wuta cikin dogon lokaci. Sanarwar ta kalubanci bangarori daban daban da su bude hanyoyi nan da nan da ake bi wajen ba da agajin jin kai yadda ya kamata.

Bayan haka sanarwar ta nuna bakin ciki ga duk irin karfin soja da ake yi wa ma'aikatan majalisar dinkin duniya, kuma ta yi kira ga bangarori daban daban da su ba da tabbaci ga zaman lafiyar ma'aikatanta da gine-ginenta. (Halilu)