Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-07-31 11:09:11    
Gamayyar kasa da kasa ta yi Allah wadai da hare-hare da sojojin sama na  Isra'ila suke kaiwa a kan kauyen Lebanon

cri

Ran 30 ga wata da asuba, sojojin sama na kasar Isra'ila sun kai hare-hare a kan kauyen Qana da ke kudancin kasar Lebanon, inda farar hula suka rasa rayukansu, wasu kuma suka jikkata. A wannan rana, bi da bi gamayyar kasa da kasa sun la'anci wannan wadarin aiki da sojojin Isra'ila suka yi. Bisa wani labarin daban da aka bayar, an ce, a ran 31 ga wata da sassafe, kasar Isra'ila ta amince da dakatar da kai hare-hare kan kudancin kasar Lebanon daga sararin sama a cikin kwanaki biyu, don yin binciken al'amarin kauyen Qana da jigilar kayayyakin agaji na jin kai zuwa kudancin kasar Lebanon cikin sauki.

Kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya ya shirya taron gaggawa a kan halin da ake ciki a kasar Lebanon a wannan rana. A cikin sanarwar da shugaban taron ya bayar, an nuna matukar mamaki da bakin ciki ga al'amarin kauyen Qana, amma ba a yi kira ga kasashen Isra'ila da Lebanon da su tsagaita bude wuta a tsakaninsu nan da nan ba. A lokacin da Kofi Annan, babban sakataren majalisar ke jawabi a gun taron, da kakkausan harshe ya la'anci sojojin kasar Isra'ila sabo da hare-hare da suka kai kan kauyen Qana da kuma babbar hasarar rayukan mutane da jima musu raunuka. A sa'i daya, ya yi kira ga kasashen biyu da su tsagaita bude wuta a tsakaninsu nan da nan.

Malam Liu Jianchao, kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin ya bayyana cewa, da kakkausan harshe, kasar Sin ta la'anci hare-hare da sojojin kasar Isra'ila suka kai, kuma da babbar murya ta yi kira kasashen Lebanon da Isra'ila da su tsagaita bude wuta a tsakaninsu ba tare da wani sharadi ba, don kaucewa wahalhalu da ake kara haddasawa.

Madam Benita Ferrero Waldner, wakilin kwamitin kungiyar tarayyar Turai mai kula da huldar waje da manufar makwabtaka ta Turai ta bayar da sanarwa inda ta yi kira ga kasashen Lebanon da Isra'ila da su daina nuna karfin soja a tsakaninsu nan da nan. (Halilu)