Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-07-30 20:55:01    
Iran ta yi wa kwamitin sulhu kashedin cewa kada ya amince da kudurin ' yin adawa' da Iran

cri

Yau Lahadi, a Teheran, kakakin ma'aikatar harkokin waje na Iran Mr. Hamid Asefi ya yi kashedi cewa, idan kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya amince da daftarin kudurin neman Iran da ta dakatar da shirinta na inganta sinadarin uranium, to Iran ba za ta sake yin la'akari da shirin da kasashe 6 suka fito da shi game da yadda za a daidaita maganar Nukiliya.

A wannan rana, Mr. Asefi ya fadi, cewa babu wata kasa da za ta iya durkusar da Iran ta hanyar matsa mata lamba ba. Sa'annan ya yi kashedi, cewa mai yiwuwa ne kasar Iran za ta dakatar da aiwatar da manufarta game da harkokin nukiliya kuma ta mayar da martani kamar yadda ya kamata idan kwamitin sulhun ya amince da shirin yin adawa da Iran. Ra'ayoyin bainal jama'a sun yi hasashen, cewa mai yiwuwa ne Iran za ta daina yin hadin gwiwa tare da hukumar makamashin nukiliya ta kasa da kasa kuma za ta janye jikinta daga ' Yarjejeniyar rashin yaduwar makaman nukiliya'. ( Sani Wang )