Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-07-23 12:45:37    
Wani jami'in Afirka ya ce, kasashen Afirka suna samun moriya sakamakon bunkasuwar dangantakar abokantaka a tsakaninsu da kasar Sin

cri
A ran 22 ga wata, Mr. Soumana Sacko, babban sakatare mai zartaswa na asusun "Afirca Capacity Building Foundation, wato ACBF ya kai suka kan magana, wai cewar "Kasar Sin tana sa Afirka da ta zama yankin mulkin mallaka" da kafofin watsa labaru na kasashen yammacin duniya suka yi. Mr. Sacko ya ce, Afirka tana samun moriya sakamakon bunkasuwar dangantakar abokantaka irin ta hadin guiwa sosai a tsakaninta da kasar Sin.

A wannan rana, lokacin a yake ganawa da manema labaru, Mr. Sacko ya nuna cewa, wasu kafofin watsa labaru na kasashen yammacin duniya sun ce, kasar Sin tana fitar da leburorinta da suke samun albashi kadan zuwa kasashen Afirka lokacin da take gina ayyukan yau da kullum a kasashen Afirka. Wannan ya sa mutane da yawa na kasashen Afirka su rasa aikin yi. Amma a hakika dai, jarin da kasar Sin ta zuba a nahiyar Afirka ya kirkiro guraban aikin yi da yawa ga mutanen kasashen Afirka. A sa'i daya kuma, kasar Sin tana taimaka wa kasashen Afirka kan yadda za a kara yin aikin raya albarkatun kwararru a Afirka, inda kasar Sin ta riga ta horar da kwararru da yawa na Afirka wadanda suka kware sosai kan fannoni iri iri.

Bugu da kari kuma, Mr. Sacko ya ce, lokacin da ake daidaita harkokin siyasa, kasar Sin ta girmama wa kasasashen Afirka da gwamnatocinsu kwarai. Kasar Sin tana sa kaimi kan kasashen Afirka a kullum, amma ba ta yi wa kasashen Afirka horo da karfi ba. (Sanusi Chen)