Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-07-21 11:58:07    
Kasar Iran ta sanar da cewa, za ta fitar da makamashin nukiliya, kuma za ta ba da amsa kan shirin kasashe 6

cri
Ran 20 ga wata, kasar Iran ta sanar da cewa, za ta fitar da makamashin nukiliya a cikin kasar, kuma da farko ta tabbatar da cewa, za ta ba da amsa kan shirin da kasashe 6, wato kasashen Amurka, da Rasha, da Sin, da Ingila, da Faransa, da Jamus suka gabatar game da warware matsalar nukiliya ta kasar Iran a ran 22 ga watan Agusta.

A wannan rana, a cikin sanarwar da ya bayar, Ali Larijani, babban wakilin shawarwarin nukiliya na kasar Iran ya yi bayani kamar haka. Bayan haka kuma, ya nuna cewa, kasar Iran tana fatan warware matsalar ta hanyar yin shawarwari, amma kasar Amurka tana da nufin kawo cikas a cikin shawarwarin, idan kasar Iran ta fuskanci fursasawa, to za ta sake yin tunani kan manufar nukiliyarta.

A wannan rana kuma, kasashe 3, wato kasashen Ingila, da Faransa, da Jamus, wadanda ke wakiltar kungiyar tarayyar kasashen Turai sun bayar da wani shirin kuduri dangane da matsalar nukiliya ta kasar Iran ga kasashen mambobi na kwamitin sulhu na M.D.D., kuma sun bayyana cewa, suna fata kwamitin sulhu zai iya zartas da shi da sauri. Shirin kudurin ya karfafa yin kira ga kasar Iran da ta daina duk ayyukan da ke da nasaba da inganta sinadarin uranium. Bayan haka kuma, shirin kudurin ya bukaci babban direktan hukumar makamashin nukiliya ta duniya da ya gabatar da rahoto kafin karshen watan Agusta, kuma ya yi bayani kan halin hadin kai a tsakanin kasar Iran da hukumar makamashin nukiliya, da kuma tafiyar da kudurin nan. (Bilkisu)