|
|
|
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye | more>> |
|
|
|
|
|
|
|
(GMT+08:00)
2006-07-19 11:53:36
|
|
Kasar Iran tana fatan samun ci gaba wajen shawarwarin nukiliya da ake yi a tsakaninta da kungiyar tarrayar kasashen Turai
cri
Ran 18 ga wata, Mahmud Ahmadinejad, shugaban kasar Iran ya ce, kasarsa tana fatan samun ci gaba kan matsalar nukiliya ta kasar Iran ta hanyar yin shawarwari da kungiyar tarrayar Turai.
A wannan rana a gun babban taron wakilan daliban kasar Iran, Mr. Ahmadinejad ya yi jawabi cewa, yin amfani da fasahar makamashin nukiliya wani iko ne na kasar Iran da ba a iya kwacewa ba, amma a sa'i daya kuma, kasar Iran tana fatan samun ci gaba kan matsalar nukiliya ta kasar Iran ta hanyar yin shawarwari da kungiyar tarrayar Turai, da kuma yin amfani da fasahar makamashin nukiliya cikin lumana a cikin filin da hukumar makamashin nukiliya ta duniya ta kayadde. Ya jadadda cewa, bai kamata kasar Amurka ta kawo matsaloli a cikin gudanarwar ba, sabo da za ta sanya a samu da bambancin ra'o'yi a tsakanin bangarori daban daban da ke cikin shawarwarin. Haka kuma, za a kawo tasiri ga bangarorin da ke da nasaba da matsalar nukiliya ta Iran. (Bilkisu)
|
|
|