Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-07-13 21:23:20    
Shugaban Iran ya yi gargadin daina yin hadin kai da hukumar IAEA

cri
Ran 13 ga wata, shugaban kasar Iran Mr. Mahmud Ahmadinejad ya yi gargadi cewa, bayan da taron ministocin harkokin waje na kasashen Rasha da Amurka da Sin da Birtaniya da Faransa da Jamus ya tsai da kudurin sake gabatar da batun nukiliya na kasar Iran ga kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, mai yiwuwa ne kasar Iran za ta yi kwaskwarima kan manufofin da take bi wajen yin hadin gwiwa da Hukumar Makamashin Nukiliya ta Duniya wato IAEA.

Mr. Ahmadinejad ya bayyana a ran nan cewa, yanzu kasar Iran tana bin hanyar zaman lafiya, wadda take karkashin 'yarjejeniyar rashin habaka makaman nukiliya' da shugabancin hukumar IAEA. Idan kasar Iran tana ganin cewa, kasashen yamma ba su nuna mata fatan alheri ba, za ta canja manufofin da take bi a yanzu. Ya kuma nanata cewa, kasar Iran tana girmama dokoki da ka'idojin duniya, amma ko kusa ba za ta yi watsi da ikon samun fasahar nukiliya ba.

Ban da wannan kuma, Mr. Ahmadinejad ya yi bayanin cewa, ya zuwa yanzu kasar Iran tana yin la'akari da sabon shirin da kasashe 6 suka bayar, za ta kuma ba da amsarta kafin ran 22 ga watan Agusta.(Tasallah)