Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-07-12 20:53:54    
Kasar Iran tana fatan yin bayani kan abubuwan da ba a tabbatar da su ba da ke cikin shirin da kasashe 6 suka bayar

cri
Ran 12 ga wata, mataimakin ministan harkokin waje na kasar Iran Mr. Manouchehr Mohammadi ya bayyana cewa, kafin za a yi bayani kan abubuwna da ba a tabbatar da su ba da ke cikin shirin da kasashe 6 suka gabatar, kasashen yamma sun bukaci kasar Iran da ta ba da amsa cikin sauri, wannan zai kawo mummunan sakamako.

A ran nan Mr. Mohammadi ya yi wa kafofin yada labaru cewa, ya kamata kasashen yamma su yi hakuri, kada su matsa wa kasar Iran lamba kan batun nukiliya na kasar Iran. Ya kamata ta hanyar yin shawarwari ne a yi bayani kan abubuwan da ba a tabbatar da su ba da ke cikin shirin da kasashe 6 suka bayar tun da wuri. Idan shirin da kasashe 6 suka bayar zai girmama ikon kasar Iran a fannin nukiliya, to, kasar Iran za ta amince da shi. Ya kuma jaddada cewa, kafin za a gabatar da abubuwan da ke cikin shirin kasashe 6 ga kasashen duniya a hukunce, za a iya yin kwaskwarima kan wasu abubuwan da ke cikin wannan shiri.(Tasallah)