Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-07-04 14:34:14    
Dukkan jiragen kasa uku sun isa birnin Lasa lami lafiya

cri

A ran 3 ga wata, dukkan jiragen kasa da suka tashi daga babban birnin kasar Sin Beijing da birnin Chengdu da ke kudu maso yammacin kasar Sin da birnin Lanzhou da ke arewa maso yammacin kasar Sin sun isa birnin Lasa lami lafiya, wannan shi ne karo na farko da jiragen kasa suka isa birnin Lasa.

A ran nan, jiragen kasa uku sun dauke 'yan yawon shakatawa kimanin dubu 3 zuwa birnin Lasa. Mazaunan kauyuka na karkarar birnin Lasa sun bayyana cewa, sun karbi 'yan yawon shakatawa da su zauna a cikin gidansu, wannan ya sa su sami moriya daga yawon shakatawa.

A ran 1 ga wata, an kawo karshen aikin gina hanyar dogo ta jiragen kasa da ke ratsa tudun Qinghai-Tibet. A sakamakon haka, birnin Lasa zai karbi 'yan yawon shakata da yawa a ko wace rana, mazaunan birnin Lasa tare da dukkan yankunan Tibet za su samu moriya daga yawon shakatawa.(Danladi)