Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-07-01 17:08:25    
Kamata ya yi shirin daidaita batun nukiliyar Iran ya kunshi muhimman abubuwa biyu, in ji ministan harkokin wajen Iran

cri
A jiya ran 30 ga watan Yuni, ministan harkokin waje na Iran, Manouchehr Mottaki ya cewa, kamata ya yi shirin daidaita batun nukiliyar Iran ya kunshi muhimman abubuwa biyu, wato amincewa da kuma tabbatar da hakkin kasar Iran da kuma inganta tsarin hana habaka makaman nukiliya.

Mr.Mottaki ya yi wannan kalami ne a yayin da yake hira da manema labaru a lokacin da yake halartar taro a hedkwatar MDD da ke birnin New York. Mr.Mottaki ya bayyana cewa, idan bangarori biyu da ke halartar shawarwarin batun nukiliyar Iran za su iya cimma daidaito a kan wadannan abubuwa biyu, to, za a iya kawar da damuwar bangare daya, a sa'in da ake tabbatar da hakkin bangare daban,

Mr.Mottaki ya kuma jaddada cewa, a ganin Iran, jerin shirye-shiryen da kasashen Amurka da Rasha da Sin da Birtaniya da Faransa da Jamus suka gabatar yana da kyau, sabo da ya koma da batun nukiliyar Iran a karkashin tsarin hukumar makamashin nukiliya ta duniya daga MDD.(Lubabatu Lei)