Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-06-29 20:57:44    
Mr Larijani zai yi shawarwari da Mr Solana a makon gobe

cri

A ran 29 ga wata, sakataren babban kwamitin zaman lafiya na kasar Iran kuma wakili na farko dangane da yin shawarwari a kan matsalar nukiliya ta kasar Iran Ali Larijani ya bayyana cewa, a makon gobe zai je kasar Spain domin yin shawarwari da babban wakili na manufofin diplomasiyya da zaman lafiya na kungiyar EU Javier Solana a kan matsalar nukiliya ta kasar Iran.

Kamfanin dillancin labaru na IRNA na kasar Iran ya ambato maganar da Mr Larijani ya yi cewa, kasar Iran za ta yi shawarwari da Mr Solana a kan matsalar nukiliya ta kasar Iran a cikin makonni biyu masu zuwa. Ya ci gaba da cewa, kasar Iran ba ta kula da kayyaden lokaci da kasashen yamma suka yi wa kasar wajen ba da amsa ga sabon shirin da kasashe 6 suka gabatar ba. Amma ya karfafa cewa, ba za a iya warware matsalar nukiliya ta kasar Iran cikin gaggawa ba.

Game da haka, kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin Malama Jiang Yu ta bayyana a ran nan cewa, yin shawarwari na diplomasiyya ya zama wata zabi na gaskiya domin warware matsalar. Kasar Sin tana fata kasar Iran za ta mai da hankali sosai a kan kulawar kasashen duniya, za ta gama kanta sosai da hukumar IAEA, haka kuma kasar Sin tana fata bangarorin da abin ya shafa za su yi hakuri, kuma za su tumtubi kasar Iran cikin yakini.(Danladi)