Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-06-26 14:10:11    
Bayani game da hanyar dogo ta Qinghai-Tibet

cri
Hanyar dogo ta Qinghai-Tibet wadda tsawonta ya kai kilomita 1956 kuma ta fi tsayi daga leburin teku a duk fadin duniya ta hade birnin Xining, hedkwatar lardin Qinghai da birnin Lhasa, hedkwatar jihar Tibet mai cin gashin kanta. San nan kuma, wannan hanyar dogo ce ta fi tsawo da aka shimfida a kan wani tudu a duk fadin duniya. Yankunan da ke da dusar kankara da wannan hanyar dogo ta ratsa sun fi yawa a duk fadin duniya. Daga cikin duk tsawon wannan hanyar dogo, an riga an kammala wani sashenta da ke hade Xining da birnin Germu na lardin Qinghai da tsawonta ya kai kilomita 814 a shekarar 1984. An fara shimfida sauran sashenta, wato daga birnin Germu na lardin Qinghai zuwa birnin Lhasa na jihar Tibet da tsawonta ya kai kilomita 1142 ne tun daga watan Yuni na shekara ta 2001. A ran 1 ga watan Yuli na shekarar da muke ciki, za a fara gwajin yin amfani da wannan hanyar dogo gaba daya.

A cikin "Shirin Raya kasar Sin" da Mr. Sun Yat-sen wanda ya shugabanta gwagwarmayar juyin juya hali kuma ya kau da daular Qing, wato daukar mulkin kama karya ta karshe ta kasar Sin yau da kusan shekaru dari 1 da suka wuce ya rubuta, Mr. Sun ya taba ambata cewa, dole ne a shimfida wannan hanyar dogo ta Qinghai-Tibet. Ba da dadewa ba bayan kafuwar Jamhuriyar Jama'ar Sin, hukumomin gwamnatin kasar Sin suka fara yin nazari kan yadda za a shimfida hanyar dogo a jihar Tibet. Tun daga shekara ta 1958, an fara shimfida sashen farko na hanyar dogo ta Qinghai-Tibet. A shekara ta 1984 ce, an gama wannan sashen da ya hade birnin Xining da birnin Germu na lardin Qinghai. Amma, babu sauran hanyar da kasar Sin za ta iya zaba, sai ta dakatar da aikin shimfida sauran sashen hanyar dogo ta Qinghai-Tibet domin ba ta da isashen kudi da batutuwa yadda za a shimfida hanyar dogo a kan tudu mai tsayi da yankuna masu dusar kankara.


1  2  3