Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-06-26 12:24:23    
Kasar Iran ta yi kira ga kasashen da ke da nasaba da su yi hakuri, domin jiran amsar da kasar Iran za ta bayar game da shirin kasashe 6

cri
Ran 25 ga wata a gun taron manaman labaru da aka shirya a Teheran, Hamid-reza Asefi, kakakin ma'aikatar harkokin waje na kasar iran ya bayyana cewa, ya kamata kasar Amurka da kasashen Turai su yi hakuri, domin jiran amsar da kasar Iran za ta bayar kan shirin kasashe 6.

Mr. Asefi ya ce, shirin da kasashe 6 suka yi ya hada da abubuwan da ke bisa doka game da harkokin siyasa da na tattalin arziki, bangaren Iran yana mai da hankali sosai kan shirin nan, kuma tilas ne ya tattaunawa sosai kan abubuwan da ke cikin shirin.

A wannan rana kuma, gidan talibijin kasar Iran ya bayar da wani labari cewa, ran 24 ga wata Kazem Vaziri Hamaneh, ministan kula da harkokin man fetur ya sake nanata cewa, idan kasashen waje sun tauye moriyar kasar Iran, to kasar Iran za ta yi ramuwar gayya da man fetur. Ya ce, kasashen duniya suna bukatun albashi, ko shakka babu takunkumin da ake yi wa kasar Iran zai kawo tasiri sosai ga kasuwar man fetur ta duniya. (Bilkisu)