Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-06-23 09:49:51    
Firaministan kasar Sin ya gana da mataimakiyar shugaban kasar Afirka ta kudu

cri

A ran 22 ga wata, firaministan kasar Sin Wen Jiabao ya gana da mataimakiyar shugaban kasar Afirka ta kudu, Phumzile Mlambo-Ngcuka a birnin Capetown.

Mr.Wen Jiabao ya ce, ya sami nasarori da dama a ziyarar da ya yi a Afirka ta kudu, kuma bangarorin biyu sun kulla jerin muhimman yarjejeniyoyi. Mr.Wen ya kuma kara da cewa, kasar Sin tana goyon bayan 'shawarar kara gaggauta bunkasuwa da jin dadinta tare' ta Afirka ya kudu wadda ke da nufin neman ingiza bunkasuwar zaman al'umma da tattalin arziki, kuma tana son ba da taimako ga Afirka ta kudu a wajen bunkasa kwararru.

A nata bangaren kuma, Madam.Mlambo-Ngcuka ta ce, Afirka ta kudu ta ji dadin muhimman nasarorin da Mr.Wen ya samu a ziyararsa a kasar, kuma tana ganin cewa, jerin yarjejeniyoyin da bangarorin biyu suka kulla sun bude makoma mai kyau ga hadin gwiwar da ke tsakanin bangarorin biyu a nan gaba. Ban da wannan, Afirka ta kudu ta kuma nuna yabo da godiya ga goyon baya da taimako da bangaren Sin ya bayar, kuma tana son aiwatar da hadin gwiwa tare da Sin a fannonin bunkasa manyan ayyuka da haka ma'adinai da bunkasa kwararru da dai sauransu.(Lubabatu Lei)