Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-06-22 19:00:42    
Ya kamata a kara raya sabuwar dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a tsakanin Sin da kasashen Afirka

cri

A ran 22 ga wata, firayin minista Wen Jiabao na kasar Sin wanda ke yin ziyara a kasashen Afirka ya halarci kuma ya bayar da wani jawabi a gun taron dandalin fadin albarkacin bakinka kan cinikayyar da ake yi a tsakanin Sin da kasar Afirka ta kudu da aka shirya a wannan rana a birnin Cape Town, babban birnin kafa dokoki na kasar Afirka ta Kudu, inda filla filla ne Mr. Wen ya bayyana matakai da manufofin da kasar Sin take bi kan yadda kasar Sin take kafa da raya sabuwar dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a tsakaninta da kasashen Afirka. Yanzu ga wani bayanin musamman da wakilanmu suka aiko mana daga birnin Cape Town.

Mr. Wen ya nuna cewa, ya kamata bangarorin kasar Sin da kasashen Afirka su yi zaman daidai wa daida cikin lumana kan harkokin siyasa da neman bunkasuwa tare da moriya juna kan tattalin arziki da kuma kara yin musanye-musanye da hadin guiwa a tsakaninsu a fannonin zaman al'umma da al'adu, har su kara fahimtar juna da sada zumunta a tsakaninsu.

Mr. Wen ya jaddada cewa, ya kamata bangarorin biyu su kara yin hadin guiwa kan harkokin siyasa, musamman kan harkokin da ke shafar kasashen duniya. Mr. Wen ya ce, "Kasar Sin za ta ci gaba da magana domin samun adalci ga kasashen Afirka a dandalin kasashen duniya. Haka nan kuma, za ta ci gaba da goyon bayan kasashen Afirka da su yi kokari ba tare da kasala ba wajen kiyaye ikon mulkin kasa da 'yancin kai da tabbatar da zaman lafiya da na karko a yankuna daban-daban na Afirka. A matsayinta na zaunnaniyar memba a kwamitin sulhu na M.D.D., kasar Sin tana ganin cewa, ya kamata a kara girmama bukatu masu kima da kasashen Afirka suke nema. Kasar Sin ta ki yarda da a wulakanta kasashe marasa karfi da daukan ma'auna daban kan al'amari daya lokacin da ake daidaita maganganun kasashen duniya."

Mr. Wen ya kara da cewa, dangantakar zaman daidai wa daida da sada sahihanin zumunci da ke kasancewa a tsakanin Sin da kasashen Afirka abin koyi ne da misali ga duk fadin Duniya.

Lokacin da ya tabo magana kan hadin guiwar da ake yi kan tattalin arziki da cinikayya a tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka, Mr. Wen ya jaddada cewa, ya kamata bangarorin biyu su nemi bunkasuwa tare da moriyar juna, kuma ya kamata su kara yin hadin guiwa a tsakaninsu. Mr. Wen ya ce, "Kasar Sin za ta tabbatar da aiwatar da manufofin daina buga harajin kwastam ga kayayyakin da ake shigowa da su a nan kasar Sin daga kasashe masu tasowa ciki har da kasashen Afirka. Kuma za ta kara ba da taimako da soke basusukan da kasashen Afirka suka ci. Sannan kuma, kasar Sin za ta ci gaba da sa kaimi ga masana'antun kasar Sin da su zuba jari kuma su yi musayar fasahohin zamani a kasashen Afirka domin samun karfin tattalin arzikin kasashen Afirka. Bugu da kari kuma, kasar Sin za ta kara shigar da kayayyakin kasashen Afirka."

Mr. Wen ya bayyana cewa, a shekarar 2005, yawan kudaden cinikayya da aka yi a tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka ya kai dalar Amurka biliyan 39.8. Daga cikinsu, yawan kudaden kayayyakin da kasar Sin ta shigo da su daga kasashen Afirka ya kai dalar Amurka kimanin biliyan 21.1.

Wen Jiabao ya nuna cewa, karfafa da raya hadin guiwa irin ta sada zumunta a tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka wani zabi ne da kasar Sin ta dade take yi bisa manyan tsare-tsare. Kasar Sin tana girmama tsarin zaman al'umma da hanyoyin neman bunkasuwa da kasashen Afirka suka zaba da kansu bisa halin da suke ciki. Kasar Sin ba za ta fitar da akidojinta da hanyoyin neman bunkasuwa zuwa ga kasashen Afirka ba. Musamman Mr. Wen ya jaddada cewa, hadin guiwar da ake yi a tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka wani sashe ne na duk hadin guiwar da ake yi a tsakanin kasashe masu tasowa. Irin wannan hadin guiwa ba a rufe take ba, kuma ba ta yi adawa da bangare na uku ba. Kasar Sin da kasashen Afirka suna yin irin wannan hadin guiwa ne a bayyane bisa ka'idojin bude kofa da hada kan sauran kasashen duniya. Bangaren kasar Sin yana maraba da sauran kasashen duniya da hukumomin duniya da su shiga irin wannan hadin guiwa. (Sanusi Chen)